• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sahihanci Shi Ne Tushen Hadin Gwiwar Afirka Da Sin

by CMG Hausa
3 years ago
Afirka

Abokaina, ko kuna son cin Avacado? Kun san a nan kasar Sin ba a noma wannan nau’in ‘ya’yan marmari, saboda haka kusan ba wanda ya san shi kafin shekaru fiye da 10 da suka wuce.

Na tuna lokacin da na sayi Avacado a karon farko, ban san ya kamata a bari ya yi laushi ba kafin a ci shi. Sai na ci shi nan take bayan da na same shi, yayin da yake da tauri. Don haka ra’ayin da na samu game da Avacado a lokacin shi ne, wani nau’in ‘ya’yan marmari ne mai tsada, kuma maras dadi.

  • An Gudanar Da Dandalin Matasan Sin Da Afirka Kan Ayyukan Sa Kai

Tabbas daga bisani na san hanya mafi dacewa da ya kamata a bi wajen dandana Avacado. Kana saboda Sinawa sun kara fahimtar amfaninsa a fannin gina jiki, hakan ya sa ana shigo da karin Avacado cikin kasar Sin. Misali, a shekarar 2010, an shigo da Avacado ton 2 ne kacal cikin kasuwannin kasar Sin, amma zuwa shekarar 2018, wannan adadi ya karu zuwa ton 43,860, inda darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 133.

Ban da wannan kuma, tun daga shekarar bana, kasar Sin ta fara shigo da Avavado daga wasu kasasahen Afirka, irinsu Kenya da Tanzania.

Hakan na daga cikin matakan da aka dauka na cika alkawarin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a wani taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, wanda ya gudana a bara, wato “Ba da sauki ga shigowar amfanin gonan Afirka cikin kasuwar kasar Sin, kana da kokarin shigo da kayayyakin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 30 daga kasashen Afirka, cikin shekaru 3 dake tafe.”
Me ya sa kasar Sin ke neman shigo da karin kayayyaki daga nahiyar Afirka? Dalili shi ne, kasar Sin na neman daidaita cinikayyar da ake yi tsakaninta da kasashen Afirka.

LABARAI MASU NASABA

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Bayanan da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta gabatar sun nuna cewa, ana samun daidaito tsakanin bangarorin Sin da Afirka ta fuskar ciniki.

Sai dai idan an tantance bayanai game da daidaikun kasa dake nahiyar Afirka, za a ga wasu kasashe na fitar da dimbin kayayyaki zuwa kasar Sin, yayin da wasu ba su samun damar fitar da kayayyakinsu sosai. Saboda haka, don raba moriya ga wadannan kasashe, kasar Sin ta dauki matakin shigo da karin kayayyakinsu.

Matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka a shekarun nan, sun hada da gudanar da tarukan baje kolin kayayyakin Afirka a kasar Sin, da kafa cibiyoyin nuna kayayyakin Afirka a wasu biranen kasar, da shirya bukukuwan tallace-tallacen kayayyakin Afirka a dandalin sayar da kaya ta kafar yanar gizo ta Internet, da samar da rance ga wasu kamfanonin kasar Sin domin su shigo da karin kayayyaki daga kasashen Afirka, da dai sauransu.

Kana sabbin matakan da kasar Sin ta dauka a bana, sun hada da fara shigo da Avacado daga kasashen Afirka, da yafe wa karin wasu kasashe mafi rashin karfin tattalin arziki harajin da ake karba bisa kayayyakin da suke fitarwa zuwa kasar Sin, wadannan kasashe sun hada da Benin, da Burkina Faso, da Guinea Bissau, da Lesotho, da Malawi, da Sau Tome da Principe, da Tanzania, da Uganda, gami da Zambia.

Wadannan matakai sun nuna yadda kasar Sin take da sahihanci, yayin da take hadin gwiwa tare da kasashen Afirka. Idan ana son kulla huldar hadin kai mai dorewa, dole ne a kulla huldar cin gajiyar juna. Sai dai ta yaya za a iya tabbatar da hakan? Amsa ita ce ta yin mu’ammala cikin daidaito, da daidaita matakai akai akai, ta yadda za a iya tabbatar da daidaituwar moriyar bangarori daban daban, da sanya kowa ya gamsu.

Wannan ma dalili ne da ya sa kasashen Afirka, ba sa amincewa da wasu maganganu marasa kyau da wasu kasashe suka fada, game da huldar hadin gwiwar Afirka da Sin.

Kasashen Afirka sun ga sahihancin da kasar Sin ta nuna, kuma sun san duk wata matsalar da aka samu, yayin da ake hadin kai da kasar Sin, za a iya warware ta ta hanyar mu’ammala, da daidaita manufofi. Saboda haka, ba su damuwa game da huldar hadin kai da suka kulla tare da kasar ta Sin. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu
Daga Birnin Sin

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Next Post
2023: Buhari Ya Hori Jami’an Tsaro Su Zama ‘Yan Ba Ruwanmu A Siyasa

2023: Buhari Ya Hori Jami'an Tsaro Su Zama 'Yan Ba Ruwanmu A Siyasa

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025
Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

November 6, 2025
Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato

An Kama Wani Mutum Kan Zargin Kashe Matarsa A Sakkwato

November 6, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karɓo Rancen N1.15trn Don Cike Giɓin Kasafin Kuɗin 2025

November 6, 2025
Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

November 6, 2025
Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

November 6, 2025
Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.