Fa’idar Sahur
1. Yin sahur koyi ne da annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam), kuma malamai sun yi ijma’i a kan mustahabbi ne yinsa kamar yadda Ibnul Munzir da Imamu Annawawi suka naÆ™alto.
2. Yin sahur saÉ“a wa Yahudu da Nasara ne, domin su ba sa yin sahur a azuminsu kamar yadda Muslim da Abu Dawud Tirmizi da Nasa’i suka ruwaito.
3. Sahur albarka ne ga mai yinsa kamar yadda hadisi ya gabata.
4. Sahur yana samar da karfi ga mai azumi wajen yin ibada, da kuma Æ™aruwar nishadi, da kuma tunkuÉ—e mummunar dabi’a da yunwa take haifarwa. Kuma a lokacin yinsa sahur, mutum yana samun dama ya yi sadaÆ™a ga almajiri ko kuma su ci tare. kuma yana sa mutum ya yi zikiri da addu’a, domin lokacin ne da ake karbar addu’a… “kamar yadda Hafiz Ibnu Hajar ya bayyana a littafinsa Fathul Bari (4/496) da malaminsa Ibnu Mulaƙƙin a cikim al’I’ilamu (5/187)
5. Samun salati daga Allah da mala’ikunsa.
Allah ya datar da mu ga koyi da Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam) a cikin al’amuranmu baki daya.