Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Andries Iniesta, ya bayyana cewa idan shugabannin kungiyar suna son gyara kungiyar ta koma kamar yadda take a baya sai an sayar da rabin ‘yan wasan kungiyar an sayo wasu.
Kakar kwallon kafa ta bana ta nuna rashin kokarin Barcelona a gasar cikin gida, amma tana haskakawa a gasar cin kofin zakarun turai ta Champions League ta kakar wasa ta 2020 zuwa 21 wadda ake bugawa.
Kungiyar ta Barcelona tana yin rashin nasara a hannun kungiyoyin da bai kamata su doke ta ba a bana da hakan ke nuna cewar abune mai wahala idan tana cikin wadanda ake sa lashe kofin La Liga na bana.
Ranar Asabar Barcelona ta buga wasa 2-2 da kungiyar kwallon kafa ta Balencia a gasar La liga lamarin da ya sanya har yanzu kungiyar take baya duk da cewa tana da kwantan wasanni guda biyu wadanda bata buga ba.
Barcelona tana tare da shugaba na rikon kwarya wanda ke son ragamar mulkin nan gaba, bayan da kungiyar ke fuskantar kalubalen biyan albashi, sakamakon matsin tattalin arziki da cutar korona ta haddasa.
Kawo yanzu Barcelona tana ta biyar a teburin La Liga da maki 21, bayan buga wasa 13 a kakar bana bugu da kari kungiyar wadda mai koyarwa Ronald Koeman ke jan ragama ta ci wasa biyar a La Liga da canjaras uku da rashin nasara hudu da kwantan wasa biyu.
Barcelona ta yi rashin nasara a wasanni da dama a bana kamar yadda ta yi a shekarar 2017 zuwa 2018 da kuma 2018 zuwa 2019 a La Liga, yayin da ta yi rashin nasara a wasa uku ta kuma lashe kofin a shekarar 2018 zuwa 2019.
Sai dai kuma Barcelona tuni ta kai zagaye na biyu a gasar Champions League ta bana da maki 15, yayin da Juventus tayi ta daya da maki 15 a rukuni na bakwai kuma yanzu Barcelona zata fafata da PSG a wasan zagaye na gaba.
A kakar shekarar 2003 Enric Reyna shi ne ya rike Barcelona a matakin rikon kwarya, bayan da Joan Gaspart ya yi murabus daga baya Radomir Antic ya maye gurbin Louis ban Gaal a matakin koci.
A waccan kakar Barcelona ta fuskanci kalubalen samun gurbin shiga gasar UEFA Cup, inda kungiyar ta sa kwazo ta kuma samu gurbin a wasan karshe da ta buga sannan kuma a lokacin Laporte ya kalli karawar a matakin shugaban kungiyar a lokacin da ya ci zabe ya zama jagora na hudu a kungiyar a kakar.
A kakar wasa ta 2020 zuwa 21 za ta kammala ne da shugaba uku, bayan Josep Maria Bartomeu sai Carles Tuskuets na rikon kwarya da wanda za a zaba ranar 24 ga watan Janairun shekara ta 2021.