• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sai An Sha Wuya A kan Sha Dadi

by CMG Hausa
3 years ago

Sanin kowa ne cewa, duk kasar dake fatan samun ci gaba har ma a rika jin amonta a duniya, wajibi ne al’ummarta su zage damtse wajen ganin wannan buri ya tabbata.

Kamar sauran al’ummomin kasashen duniya, al’ummar Sinawa sun hada karfi da karfe wajen gina kasar Sin mai bin tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin a sabon zamani.

  • Babu Nasara Ga ’Yan Awaren Taiwan

Gagarumin ci gaban da kasar Sin ta cimma a cikin shekaru 10 da suka gabata (2012-2022), sun hada da fannonin tattalin arziki, da binciken sararin samaniya, da fannin kirkire-kirkire da inganta muhalli da zaman rayuwar jama’a da sauransu.

Bayanai na cewa, karfin tattalin arzikin kasar Sin ya kai wani sabon matsayi, ma’aunin GDPn kasar ya kai Yuan triliyan 114, adadin da ya kai kashi 18 bisa dari na karfin tattalin arzikin duniya, wanda bai wuce kashi 11.4 bisa dari ba a shekarar 2012. Masu iya magana na cewa, idan ka ga wane ba banza ba.

A wadannan shekaru, kasar Sin ta ba da gudummawar kashi 30 bisa dari ta fuskar bunkasuwar tattalin arzikin duniya, wadda ta kasance babbar kasar dake taimakawa karuwar tattalin arzikin duniya. Kana ta yi nasarar warware babbar matsalar fama da kangin talauci, wadda ta damu jama’ar Sin cikin dubban shekaru a baya.

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

Yanzu haka, akwai mazauna kauyuka kimanin miliyan 98.99 da suka yi ban kwana da kangin talauci. Adadin kauyukan da suka sauya zuwa birane, ya karu daga 53.1% zuwa 64.7%. Mazauna kauyuka kimanin miliyan 180 sun kaura zuwa birane.

A matsayinta na kasar dake kan gaba wajen yawan masu amfani da intanet a fadin duniya, kuma daya daga cikin bangaren da kasar ta samu gagarumin nasara, kasar Sin na kan hanyar sauyawa daga yawan adadi zuwa raya harkar intanet mai inganci, da gina tsarin tafiyar da yanar gizo mai cike da tsaro, sakamakon kyautatuwar ababen more rayuwa masu inganci, da ci gaban fasaha da bunkasar tattalin arziki na zamani. Hakika kasar Sin ta ciri Tuta.

Tsakanin wadannan shekaru da muke batu, adadin masu amfani da yanar gizo a kasar Sin, ya karu daga miliyan 564 zuwa fiye da biliyan 1.03, abin da ya sanya ta zama matsayi na daya a duniya. Kasar Sin ta samar da manyan hanyoyin sadarwa na 5G da layin fiber optic mafi girma a duniya. Kuma duniya ta shaida wannan nasara.

Darajar tattalin arzikin zamani na kasar Sin, ta tashi daga kudin Sin RMB yuan tiriliyan 11 kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 1.6 a shekarar 2012 zuwa yuan tiriliyan 45.5 a shekarar 2021, wanda ya sanya ta ci gaba da zama kasa ta biyu a duniya a cikin shekaru da dama a jere.

Yawan jimillar tattalin arzikin zamani a GDPn kasar, shi ma ya karu daga kashi 21.6 cikin 100 a shekarar 2012 zuwa kashi 39.8 cikin 100 a shekarar 2021.

Hada-hadar cinikayyar Intanet ta kasar Sin da tsarin biyan kudi ta wayar salula, duk sun kasance a kan gaba a duniya.

Nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannoni daban-daban, a wadannan shekarun da suka gabata, ba nasara ce kawai ga kasar Sin kadai ba, nasara ce ga duniya baki daya.

Hakan ya kara jaddada cewa, sai an zubar da ruwa a kasa kafin a taka damshi. (Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

October 17, 2025
Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika
Daga Birnin Sin

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Taya Hukumar FAO Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwa

October 16, 2025
Next Post
Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Alluran Rigakafin COVID-19 Ta Haifar Da Kyakkyawan Sakamako

Hadin Gwiwar Sin Da Afirka A Fannin Alluran Rigakafin COVID-19 Ta Haifar Da Kyakkyawan Sakamako

LABARAI MASU NASABA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

October 17, 2025
Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

October 17, 2025
A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho

Zan Tabbatar Ana Tafiyar Da Ayyuka A Tashoshin Jiragen Ruwa A Afrika Ta Yamma —Dantsoho

October 17, 2025
Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

October 17, 2025
peter

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

October 17, 2025
Ƙungiyar NNYLF Ta Gargaɗi Atiku Da Sowore Kan Cinna Wutar Rikici A Nijeriya

Ƙungiyar NNYLF Ta Gargaɗi Atiku Da Sowore Kan Cinna Wutar Rikici A Nijeriya

October 17, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci

October 17, 2025
Tinubu

Batun Yin Afuwa Ga ‘Yan Yankin Ogoni Huɗu

October 17, 2025
Shettima

‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima 

October 17, 2025
Manzon Allah

Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya

October 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.