Umar A Hunkuyi" />

Sakamakon Ganawar Da Buhari Ya Yi Da Kwamitinsa Na Yaki Da Cin Hanci…

•Ya Umurci Hukumomin Yaki Da Cin Hanci Su Sayar Da Duk Kadarorin Da Suka Kama

•Kwamitin Ya Ayyana Bankado Kadarori Na Fiye Da Naira Tiriliyan Daya

•Yaki Da Cin Hanci Ba Zai Yi Nasara A Nijeriya Ba Sai Da Hadin Kan Talakawa

A ranar Alhamis ce, Shugaba Buhari ya gana da wakilan kwamitin bayar da shawara na shugaban kasa a kan yaki da cin hanci da karban rashawa (PACAC).

Taron wanda aka fara shi da misalin karfe 11:30 na safiya a fadar ta shugaban kasa.

Kwamitin na PACAC, wanda aka kafa shi a watan Agusta na shekarar 2015, shi ne kwamiti na farko wanda shugaba Buhari ya kafa bayan hawansa karagar mulkin kasar nan a ranar 29 ga watan Mayu, 2015.

An dorawa kwamitin nauyin samarwa da gwamnati yanda za ta yaki matsalar cin hanci da karban rashawa ne.

Ana kuma sa ran kwamitin ya baiwa gwamnati shawara a kan yanda za ta yi hukunci ne a kan yaki da cin hanci da karban rashawa din.

Kwamitin na PACAC, yana samun goyon baya ne daga wani kwamitin mai wakilai Bakwai.

A yayin ganawar, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umurci hukumomin da ke yako da cin hanci da rashawa su sayar da dukkan kadarorin da suka kwace daga hannun mutanen da ake zargi da handama da babakere da dukiyar kasa.

Buhari ya ce idan an sayar da kadarorin a zuba a cikin asusun gwamnatin kasa daya tilo da take amfani da shi.

Wannan na zuwa ne a sa’ilin da kwamitin bai wa shugaban kasan shawara kan yaki da cin hanci ya bayyana cewa ya bankado kadarorin da wasu suka handame daga dukiyar kasa da kudinsu ya kai kimanin Naira Tiriliyan daya, kuma an yi amfani da kudin a wasu shirye-shirye na gwamnati na kyautata walwalar jama’a da kuma ciyar da dalibai a makarantu.

Shugaban Kwamitin, Farfesa Itsey Sagay ya kuma ce a halin yanzu yakin da suke yi da cin hanci da rashawa zai fi mayar da hankali ne a tsakanin manyan jami’an gwamnati.

A lokacin da yake tarbar kwamitin, Shugaban Kasa Buhari ya yi alkawarin duba hanyoyin da za a bi a rage yawan kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da harkokin gwamnati.

Sanarwar da mai bai wa shugaban kasan shawara kan yada labaru, Femi Adesina ya fitar, ta ce Shugaba Buhari ya gode wa kwamitin bisa namijin kokarin da yake yi kan yaki da cin hanci, kana ya ce ba karamar sadaukarwa ga kasa suka yi ba wajen amincewa su gudanar da wannan jan aikin, yana mai cewa, “na san wasu daga cikin manyan kasa ba za su amince da ku ba, kuma ba za su so ku ba ko da makusantanku ne shakikai,” in ji sanarwar.

A halin da ake ciki kuma, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban kwamitin bai wa shugaban kasa shawara a kan yaki da cin hanci da rashawa, Farfesa Itse Sagaya sun yi kira ga ‘Yan Nijeriya su shiga sosai a dama da su a yakin da ake yi da cin hanci domin ci gaban kasa.

Sun bayyana cewa gwamnati ita kadai ba za ta iya samun nasara dari bisa dari ba, ba tare da samun goyon bayan talakawa ba

Bakidayansu, sun nemi hakan ne a yayin da suke jawabi a wajen kaddamar da wata manhaja ta yaki da cin hanci mai lakabin ‘flag it’ wanda Gidauniyar Akin Fadeyi tare da hadin gwiwar Hukumar Kiyaye Hadurran Kan Titi ta Kasa (FRSC) suka samar, a Cibiyar Tunawa da Shehu Musa ‘Yar’Adua da ke Abuja.

Mataimakin shugaban kasa Osinbajo, wanda mai bai wa ofishinsa shawara ta musamman a kan bin doka, Fatima Waziri-Azi ta wakilta, ya jaddada cewa ya kamata a samu wani kyakkyawan kawance a tsakani gwamnati da al’umma matukar ana so a samu nasarar yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan.

Exit mobile version