Babban sakataren kungiyar kasashe masu arzikin man fetur (OPEC), Mohammed Sanusi Barkindo, ya rasu.
Mele Kyari, Manajin Darakta na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) Limited, ya sanar da rasuwarsa a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter da sanyin safiyar ranar Larabar nan.
Kyari ya ce ya rasu ne da misalin karfe 11 na daren ranar Talata ‘yan sa’o’i kadan bayan ya gabatar da jawabi ga masu ruwa da tsaki a harkar man fetur da iskar gas a taron da aka gudanar kan sanin mai da iskar gas na Nijeriya na shekarar 2022 da aka gudanar a Abuja.
Bayan kammala taron ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati tare da tawagar sakatariyar kungiyar OPEC.
Ya rasu yana da shekaru 63.
“Za a sanar da shirye-shiryen jana’izar sa nan ba da jimawa ba.” inji Kyari.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp