Sakataren Gwamnatin Jihar Ondo (SSG), Hon. Temitayo Oluwatuyi, wanda aka fi sani da Tuykana, ya rasu.
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa Mista Oluwatuyi ya rasu ne, a safiyar Asabar a wani asibiti da yake jinya bayan hatsarin mota da ya yi makonni biyu da suka gabata.
- Kungiyar ‘J5 Container’ Ta Gudanar Da Taron Neman Hadin Kan Jami’an Tsaro A Legas
- Manyan Batutuwa 10 Da Suka Mamaye Siyasar Nijeriya A 2024
Hatsarin ya faru ne a ranar 19 ga watan Disamban 2024, lokacin da yake tafiya zuwa Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Har yanzu gwamnatin Jihar Ondo, ba ta fitar da wata sanarwa kan rasuwarsa ba.
An naÉ—a Mista Oluwatuyi a matsayin sakataren gwamnatin jihar a ranar 24 ga watan Janairun 2024.