Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na daga cikin abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwarsa.
El-Rufai, ya bayyana hakan ne a yayin taron Arewa Tech Fest da aka gudanar a Kano ranar Laraba.
- CMG Ya Gabatar Da Bikin Baje Shirin Bidiyo A Moscow Albarkacin Bikin Cika Shekaru 75 Da Kafuwar Janhuriyar Jama’ar Sin
- Ina Dalilin Da Ya Sa Amurka Ke Shirin Daina Amfani Da Manhaja Da Injuna Kirar Sin A Motoci Masu Kama Intanet?
Taron ya tara ’yan siyasa da kwararru don tattauna ci gaban da ake samu a Arewacin Nijeriya.
Manyan mutane, ciki har da gwamnonin jihohin Kano, Katsina, da Zamfara, sun halarci taron.
El-Rufai ya ce, “Dawo da Mai Martaba kan sarautar Kano, ya kasance ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwata, kuma ina so na taya ku murna.”