Kamfanin wutar lantarki na Tokyo dake Japan ya sake gamuwa da wani lamari. Babban kamfanin samar da makamashin nukiliya mafi girma a kasar Japan, ya fada jiya cewa, mai yuwa kuskuren dan-Adam ne ya haddasa hadarin da ya faru da na’urar tsaftace gurbataccen ruwa a tashar makamashin nukiliya ta Fukushima Daiichi jiya. A lokacin, wani ma’aikaci ya gano cewa, ruwa na yoyo daga na’urar yayin da yake gogewa. Yana mai cewa, daga cikin bawuloli 16 da ya kamata a daure su da hannu yayin tsaftacewar, 10 a bude suke. Hakan ya sa ruwan dake dauke da sinadarin nukiliya, ya kwarara zuwa cikin bututun ya kuma haÉ—u da ruwan famfo.
A cewar rahotannin kafofin yada labaran kasar dake Fukushima, hadarin ya haifar da zubar a kalla tan 5.5 na gurbataccen ruwa. Kafofin yada labarai na cikin gida sun ba da rahoton cewa, matakin iska mai guba a wurin da lamarin ya faru, ya zarce sau 240 fiye da na yankin da ke kewaye.
- An Gama Aikin Bitar Liyafar Bikin Bazara Karo Na 5 Ta Kasar Sin
- Shugaban Miyetti Allah, Abdullahi Bodejo Mutum Ne Mai Yi Wa Nijeriya Fatan Alhairi
Al’ummar duniyar ba ta yi mamakin sake afkuwar wani hadari a TEPCO ba. Tun bayan hatsarin tashar makamashin nukiliya ta Fukushima a shekarar 2011, wannan kamfani ya fuskanci hadurra da badakala iri-iri daga lokaci zuwa lokaci. Amma ko shi kansa kamfanin, ba zai iya bayyana jimillar adadin ba.
Tun daga watan Agustan shekarar da ta gabata, Japan ta zubar da gurbatccen ruwan nukiliya har sau uku a cikin tekun, inda ta zubar da ruwan dagwalon nukiliya da ya kai sama da tan dubu 23. A wannan watan ne kuma, ake sa ran za a fara zagaye na hudu na zubar da ruwan dagwalon a cikin teku. Wani sabon hadarin da ya afku a TEPCO, ya sake ankarar da bangaren Japan. Don haka, ya kamata ’yan siyasar Japan su dauki alhakin lamarin, da yin taka tsan-tsan wajen tunkarar hadurran tsaron kamfanin TEPCO, da yin kira da a dakatar da tsare-tsaren fitar da hayaki mai guba nan gaba, da yin shawarwari da kasashen duniya, da samar da mafita da dukkan bangarori suka amince da shi. (Mai Fassarawa: Ibrahim Yaya)