Daga cikin dalilan da suka kara bai wa wannan hadakar kungiyoyi tamu ta masu kishin jihar Kano kwarin-gwiwar sanya na-mujiya cikin sha’anin wannan zabe na kananan hukumomi da hukumar zaben ta Kano (KANSIEC) ta gudanar, karkashin jagorancin Farfesa Sani Lawan Malumfashi, bai wuce yin maraba tare da sahalewa kungiyoyin al’umma shigowa cikin sabgar ka’in da na’in da hukumar zaben ta yi ba. A daya hannun, ta tabbata cewa, ita ma gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin maigirma Abba Kabir Yusuf, ba tai yunkurin farmakar masu sanya-idanu cikin sha’anin zabukan ba.
Batun sahalewa kungiyoyin al’umma na gida da na waje, sanya-idanu cikin sha’anin zabukan wannan kasa, wani al’amari ne mai wuyar sha’ani, musamman ga gwamnatocin da babban burinsu shi ne, su sami nasarar lashe zabuka ta kowane hali. Ba ya ga irin wadannan gwamnatoci, hukumomin zabe ma da aka nada su, kan marawa shugabannin gwamnati baya, wajen kange kungiyoyin al’umma, ga barin sanin irin wainar da ake toyawa cikin harkokin zabukan, a cikin sako da lungu na kasar.
- Okawa Bai Taimake Ni Da Kuɗin Jihar Delta Don Na Yi Kamfe A 2023 Ba – Atiku
- Ya Kamata A Dakatar Da Duk Wasu Wasanni A Sifaniya Saboda Ambaliyar Balencia – Ancelotti
Cikin zabukan Shekarar 2007, kungiyar kare hakkin dan’adam “Human Rights Watch” ta yi taro da “yan jaridu, tare da raba musu takardar bayan taro, mai taken “Election or Selection” (Zabe ko Nadi). Bugu da kari, kungiyar, ta yi kalubale ga hukumar zabe da kuma gwamnatin tarayya, tana mai zarginsu da hadin-baki tare da jan-kafa da hukumar zaben ke yi, na kin tantance kungiyoyin sanya-ido a zabe bisa lokaci, kamar yadda dokokin zaben suka lamunce.
(Daily Trust, April 5, 2007).
Har ila yau, ba ya ga gwamnatoci da hukumomin zabe, ta tabbata hatta jami’an tsaro ma na da mugun tabo, wajen nuna kyama da kuma kyarar irin wadannan kungiyoyi namu na al’umma da ke bin-diddigin batutuwan zabukan a Kasa. Cikin zabukan Shekarar 2007, an gabatar da wasu kunshin rahotannin da ke hakkake cewa, jami’an tsaro na farin kaya (DSS), sun ta kai farmaki a kan kungiyoyin sanya-idanu a zabukan Shekarar. Jami’an tsaron, na kafa hujjar cewa, wai jam’iyyun “yan adawa ne ke daukar nauyin kungiyoyin.
(Daily Trust, April 3, 2007).
A karshe, wannan hadakar kungiyoyin al’uma namu da ke rajin kishin wannan jiha tamu ta Kano, na matukar yaba irin yadda shugaban hukumar zabe ta Kano, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, ya zage dantse tare da jajircewa, wajen gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihar, duk da irin bita da kulli da ya rika fuskanta dare da rana. Ya ba da lokacinsa da ma ransa, wajen ganin ya ba da gudunmuwar samawa kananan hukumomin na Kano shugabanci nagari, wadanda jama’ar gari ke zabarsu, don gudanar musu da ayyukan da za su taba rayuwarsu tabawa.
Wadannan nasarori da shugaban hukumar zaben ya tsuwurwurta, ba su kasance nasa ne shi kadai ba, haka ba na gwamnatin Kano ba ne ita kadai. Gaskiyar magana, irin wadannan gwala-gwalan nasarori da ya girba, sun zamto ne na daukacin jama’ar jihar Kano ne baki daya. Domin kuwa, da wannan zabe ya zo da tangardar da za ta jaza salwantar rayuka da dukiyoyi, da ba wannan zance ne ake yi ba yanzu. Da mai yi wa, hatta wannan tsokaci namu ba zai rubutu ba.
Babu shakka, zai yi matukar ma’ana, ya zamana sauran hukumomin zabe da za su zo nan gaba, su zamto suna masu yin koyi ne da irin salon malaminmu Farfesa Sani Lawan Malumfashi, wajen jajurcewa tare da gudanar da ingantattun zabuka, don nasarar Jihar Kano, da ma Nijeriya bakidaya.
Kawowa Zaben Kano Tarnaki Tamkar Rashin Kishin-kai Ne
Sanin kowa ne a Kano cewa, wasu mutane sun yi yunkurin hana gudanar da zabukan kananan hukumomi da hukumar zabe ta Kano ta tasamma yi, inda suka garzaya zuwa Kotu, tare da karbo umarnin Kotu, na dakatar da duka zabukan bakidaya. Ko ma mene ne dalilin masu karar, ba shi ne abin kallo ba, a gabar da ake ciki. Kamar yaya?. Abin la’akarin shi ne, gwamnatin tarayya hada da kotun koli ta kasa, sun ci alwashin kin yarda a bai wa kowace karamar hukuma kudin wata-wata da ake ba su daga asusun tarayya, muddin ba a gudanar da zabukan kananan hukumomi a cikin Watan na Oktobar (October, 2024), da ake ta dambarwar zuwa Kotunan Shari’a a cikinsa ba, cewa, a yi zaben, koko ka da ma a yi.
Akwai masu ra’ayin cewa, yunkurin dakatar da jihar Kano aiwatar da zabukan, tamkar wani tarko ne da aka so yi wa jihar ta Kano, don ta yi adabo da wadancan kudaden na kananan hukumomi. Ba sai an yi wa mai karatu wani dogon bayani ba, rashin ci gaba da shigowar wadancan kudade, zai iya kassara rayuwar miliyoyin jama’ar Kano ta mabanbantan fuskoki. Sai wasu suka yi tsai, tare da yin jinjina ga tutsun da gwamnatin Kano da hukumar zaben suka yi, na cewa, babu makawa sai sun gudanar da zabukan, duk da cewa, ba kowa ne ya fahimci fa’idar kafiyar da suka nuna ba.
Bangaren Shari’a Kan Yi Wa Dimukradiyya Lahani
Duk da irin tsantsar muhimmancin da tsagin shari’a ke da shi karkashin tsarin dimukrradiyya, an wayigari a wannan Kasa, inda dubban mutane ke munana masa zato. Babu yadda za a yi, aji-dadin gudanar da ita kanta dimukrradiyyar, muddin za a bar jama’a su ci gaba da rayuwa sasakai, ba tare da wasu dokoki na yi musu iyaka da kuma linzami ba. Sai dai, akwai masu kokarin faiyace irin mugunyar rawar da ake zargin bangaren shari’ar Kasar ke takawa, cikin lamuran siyasar Kasar, musamman cikin wannan zubin jamhuriyar siyasa ta hudu da muke ciki. Sai aka wayigari, tamkar tsagin masu mulki ne suka fi sauran jama’ar gari amfanuwa daga bangaren na shari’a a Kasar.
Dambarwar Babban Maishari’a Katsina-alu da Shugaba Salami, 2007
Da yawan masharhanta na da tunanin cewa, zanin bangaren shari’a a Najeriya bai taba sillewa karara ba a bainar jama’a, tare da yi mata tonon sililin takan kaucewa gaskiya, cikin batutuwan siyasar wannan Kasa, irin yadda ya faru cikin Shekarar zaben 2007, tsakanin babban maishari’a na Kasa Katsina-alu, da maishari’a kuma shugaban sashen kotunan daukaka kara na Kasa, Salami, game da batun kujerar gwamnan Sokoto. Ko ba a yi wa mai karatu dalla-dalla ba, zai fahimci akwai mai son yin awon-gaba da kujerar gwamnan cikinsu, gudan kuma, na son tabbatar da ita ne (wannan haka yake).
(Source, February 21, 2011: 5, 30, 33, 3b).
Babban dalilin kawo wancan misali dake sama shi ne, akwai wadanda mamaki ya karsu cewa, ta yaya ne za a ce Kotun Koli ta yi wa’adin wajibcin gudanar da zabukan kananan hukumomin lallai cikin Watan na Oktobar 2024, amma wasu “yan siyasa, su je, su amso wata takarda daga wata kotun da ba ta kai ta koli daraja ba, wadda za ta haramta gudanar da zaben a cikin wannan Wata da ta iyakance gudanar da zabe cikinsa!
Koma mene ne mafitar gwamnatin jihar Kano da kuma hukumar zaben ta jihar, da yawan mutane na da tunanin cewa, gudanar da zabukan ne mafi a’ala sama da kin aiwatar da su. Bugu da kari, kaurin-suna da manyan kotuna da manyan alkalai suka yi a Kasar, cikin batutuwan siyasa, na daga dalilan dake sanyawa a gaza fahimtar kotunan, ko da kuwa hukuncin da suka furzar akan hanya yake.
Shari’ar Nasiru Yusuf Gawuna Da Dahiru Abdu Oska, 2007
Irin yadda batun shari’ar tsohon mataimakin tsohon gwamnan Kano, Nasiru Gawuna ta gudana, tsakaninsa da abokin bugawarsa, wato Dahiru Oska, ita ma ta bar gagarumin miki tsakanin alkalan da kuma jama’ar Kano, game da batun sabgar siyasa.
An yi waccan shari’a ne bayan kammala babban zabe na Kasa na Shekarar 2007, inda Gawuna ke yin takarar kujerar shugaban karamar hukumar Nassarawa karkashin jam’iyyar ANPP, shi kuma Oska ke yin tasa takarar ta kujerar shugabancin karamar hukumar ta Nassarawa a karkashin jam’iyyar PDP. Bayan hukumar zabe ta aiyana Gawuna a matsayin wanda ya sami nasarar lashe zaben, sai Oska ya shigar da kara kotu. Wani abin ban mamaki, sai da lokacin saukar Gawuna daga kan kujerar shugabancin karamar hukumar ya yi, sannan ne aka yanke hukunci. Sai Alkali ya tabbatar da nasarar lashe zaben ga Abdu Oska. Sai dai, ko daga garin gaba-gaba mutum ya fito, ba shi iya ba da kyakkyawar fassara ga wannan hukunci, wanda sai bayan Shekara uku ne aka iya gano cewa, Nasiru Yusuf Gawuna haramtacciyar kujerar mulki ce ya hau, wanda ba hakkinsa ba ne.
Lokaci ya yi da ya kamata bangaren na shari’a da ya tsaya ya yi karatun ta-natsu, wajen kare mutuncin kansa, da yin amai ko ruwan hukunce-hukunce bisa doron gaskiya, tare da kaucewa duk wasu burace-burace na siyasa, da za su ci gaba da afkar da munanan zato a tsakanin jama’ar gari da kotunan.