Mohammed Salah ba zai buga wasan da Liverpool za ta yi da Arsenal a gasar cin kofin FA a ranar Lahadin nan ba.
Salah dai yana tare da ‘yan wasan kasar Masar gabanin gasar cin kofin nahiyar Afrika (AFCON), masu sha’awar kallon kwallon kafar na jiran suga yadda Liverpool zata kasance ba tareda Salah ba.
- Mako 13 Ya Yi Kadan Wurin Dawo Da Birmingham Cikin Hayyacinta – Rooney
- Borrusia Dortmund Na Shirin Dawo Da Sancho Bayan Rashin Katabus A Man U
Salah ya jefa kwallaye 18 a wasanni 27 da ya bugawa Liverpool a bana, inda take a matsayi na daya a saman teburin gasar Firimiya ta bana da maki 45.
Yawancin masu horaswa a kasashen Turai suna kokawa akan yadda manyan yan wasansu kan tafi domin wakiltar kasashensu yayin da ake tsaka da gudanar da wasanni a kasashen Turai.