Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ware kudi naira miliyan 114 don raba wa matasa da mata a fadin gundumomi 114 na jihar domin su samu damar gudanar da bukukuwan babbar sallar cikin nishadi.
Shugaban Jam’iyyar APC reshen Jihar Gombe, Mista Nitte Amangal, ne ya bayyana haka a sakatariyar jam’iyyar ta jihar yayin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala wani taro.
- Cikin Shekara 3 Mun Yi Aiki Tukuru Don Ci Gaban Jihar Gombe —Inuwa Yahaya
- Hajjin Bana: NCAA Ta Ziyarci Filin Jirgin Gombe, Ta Ce Filin Zai Yi Jigilar Alhazai
Ya ce, hakan na daga cikin kudurin Gwamna Inuwa na samar da tallafi ga talakawa a lokutan bukata kamar bukukuwan sallah. Ya jaddada cewa, wannan karamci ne na musamman ga matasa da mata ne kadai, yayin da na barka da sallah na nan tafe.
Mista Nitte Amangal ya yi imanin cewa matakin zai saukaka wahalhalun da mutane da dama ke fuskanta yayin bukukuwan, musamman matasa da mata.