Rundunar ’Yansandan Jihar Kano, ta tabbatar wa al’ummar jihar cewar za ta samar da ingantaccen tsaro a lokacin bukukuwan sallah.
Kwamishinan ’Yansandan jihar, Ibrahim Bakori ne, ya bayar da wannan tabbaci yayin wata ganawa da shugabannin al’umma da ƙungiyoyin agaji da ke nuna damuwa kan yiwuwar tashin hankali yayin bukukuwan sallah.
- Sabbin Nasarorin Rigakafi Da Warkar Da Cutar TB Na Kasar Sin Sun Kara Kuzarin Dakile Yaduwarta Duniya
- Sabbin Nasarorin Rigakafi Da Warkar Da Cutar TB Na Kasar Sin Sun Kara Kuzarin Dakile Yaduwarta Duniya
Ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro na aiki tare domim daƙole tashin hankali, tare da yin kira ga jama’a su zauna lafiya da kuma bayar da rahoto kan duk wani abu da zai iya tayar da hankali.
Bakori, ya gargadi duk masu shirin tada zaune tsaye cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani abu da zai haifar da rikici ba.
Ya jaddada cewa duk wanda aka kama yana aikata abin da zai kawo ruɗani zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Ya kuma yi kira ga iyaye su kula da ’ya’yansu tare da hana su shiga ayyukan da ka iya haddasa tashin hankali.
Ya tunatar da al’umma cewa Sallah lokaci ne na zaman lafiya, haɗin kai, da farin ciki, don haka dole ne kowa ya fifita zaman lafiya fiye da bambance-bambancen da ke tsakaninsu.
Rundunar ta kuma samar da lambobin kiran gaggawa don bayar da rahoton abubuwan da ke faruwa a lokacin bukukuwan sallar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp