Mun gode wa gwamnatin tarayya ‘yan’uwa
Ta raba mu da kwakudubar bana
Ta kawo Geron taimako, ta kawo dawar taimako,
Arayye ga Garin Kuli-kuli ga Garin Kwaki,
Arayye an yi rabo na gaskiya ba a cuci kowa ba,
Ga Angurya ga Budu ta ce a bai wa dabobi,
Kusan ta gyaro Lautai,
Arayye don ga Laturu da Famfo ma an kawo,
Arayye saura Rediyo Girim mai wakar Soriye”.
Wadansu baitoci kenan a cikin wakar Soriye, wadda tsohuwar mawakiya Salmai Albasu ta rera, domin jinjina wa gwamnatin waccan lokaci; kan yadda ta kawo abubuwan more rayuwa da abinci ga takalawa, wannan waka ta yi matukar tasiri a shekarun baya, sannan har yanzu wasu gidajen rediyon kan saka ta a zabukansu; lokaci bayan lokaci.
“Shekara kwana ga mai tsawon rai”, in ji Bahaushe. Haka kuwa maganar take, domin kuwa matashiyar da ta rera dadaddiyar wakar; mai dadin sauraro a shekarun baya, mai taken Soriye, wadda kuma ta yi tasiri a kunnuwan masu sauraren wakokin Hausa, musamman a gidajen rediyo a wancan lokaci; yau ta cika shekara 70 cif a raye.
Salmai Albasu, ba sabon suna ba ne a wajen mutane masu sha’awar sauraran rediyo, musamman masu amfani da harshen Hausa, yau an wayi gari ta daina wakar amma har yanzu a kan saka wakokinta shahararru a gidajen rediyon da ke Arewacin Nijeriya.
Salmai, a wata hira da ta yi da BBC Hausa ta bayyana cewa; ita haifaffiyar Albasu ce da ke Jihar Kano, dukkanin iyayenta Katsinawa ne, amma kuma mazauna garin Albaus, ta bayyana cewa; tun a lokacin da ‘yan mata ke yin rawar dandali yayin da makada ke kida ta fara yin waka, inda a wancan lokacin take yin waka, wadansu ‘yan mata kuma ke yi mata amshi.
“Daga wasan kuruciya na ‘yan mata na fara waka, a wancan lokaci; akwai makada da dama da ke kida, ni kuma da sauran kawayena muna waka, amma ni ce nake rera wakar; su kuma suna yin amshi har ta kai ga na ci gaba da yin wakoki. Sannan, ana daukar mu zuwa Sakatariyar Karamar Hukuma, muna wayar da kan al’umma a wancan lokaci, saboda a wancan lokaci; mutane ba su waye da harkar karatun boko da sauran shirye shiryen gwamnati ba.
Wannan dalili ne yasa ake zuwa da mu gari-gari, muna yin waka mutane na jin dadi suna yi mana likin kudi muna kwasa. Haka nan, babu abin da za mu cewa waka, sai san barka; domin kuwa saboda ita na ziyarci wurare da dama a Arewacin Nijeriya, har ma da Kudanci, misali kamar Jihar Legas.
Har ila yau, dangane da makada da sauran abokan aikin Salmai a wancan lokaci, Dattijuwar ta ce akwai Sarkin makada Sule, Tunare, Shu’aibu Kwata, wanda yake maroki ne, sai kuma bangaren masu yi mata amshi akwai; Subdi da Uwani wadanda dukkansu Allah ya yi musu rasuwa.
Wakoki kamar Soriye, A kai yara makaranta, Ku san ilimi mu ji dadi da sauransu, su ne wakokin da suka fi shahara a cikin wakokin da zabiyar ta yi. Kazalika, Salmai ta bayyana cewa; a lokacin da take kan ganiyarta, ta fi mayar da hankali wajen wakokin da suka shafi cin zarafin ‘ya’ya mata da kuma na zaburar da mutane, musamman yara kanana da su nemi ilimin addini da na book, ganin yadda a wancan lokacin ake tsanar ilimin boko a Arewacin Nijeriya.
Dangane da batun ko ta samu wani a cikin ‘ya’yanta da ya gaje ta a wannan sana’a ta waka? Sai Salmai ta ce, ko kusa babu wani daga cikin yaranta su bakwai da ta haifa da ya nuna sha’awar harkar waka, hasali ma mafi yawancinsu tuni sun yi aure; sun tare a gidajen mazajensu, amma dai a cewar tata; har yanzu idan aka kunna wakokinta a gidajen rediyo, hakan na matukar saka ta farin ciki tare da tuna mata shekarun kuruciyarta.
A zamanin baya, gwamnatoci sun yi amfani da wakoki da sauran hanyoyi wajen wayar da kan mutane, musamman wadanda ke zaune a karkara, domin nusar da su muhimmancin neman ilimin addini da na boko, tsabtace wajen muhallinsu da kuma hanyoyin da za su bi wajen kare kansu daga wasu cututtuka daban-daban a wancan lokaci.