Kawo yanzu za a iya cewa babu wata gasar ƙwallon ƙafa a nahiyar Turai da take ɗaukar hankalin ƴan wasa da masu horarwa har ma da ƴan kallo kamar gasar firimiyar Ingila saboda yadda wasanni suke ƙayatarwa da kuma irin kuɗaɗen da ake kashewa.
Wannan ne ya sa masu zuba jari a ƙwallon ƙafa suke son zuba ko sayen wani kashi na ƙungiya ko kuma mallakar ƙungiyar ma gaba ɗaya a Ingila saboda yadda wasanni suke ƙayatarwa.
- Kungiyoyin Gasar Firimiya Sun Kashe Dala Biliyan 4 A Kasuwar Saye Da Sayar Da ‘Yan Kwallo Ta Bana
- Yadda Kungiyoyin Firimiyar Ingila Suka Shirya Wa Kakar Bana
An kashe kusan sama da fam biliyan uku a cinikayyar ƴan ƙwallo a gasar Premier League ta ƙasar Ingila, inda aka kammala hada-hada ranar Litinin, 01-09-2025 ɗaya ga wannan watan da muke ciki.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liɓerpool ce kan gaba a yawan kashe kuɗi inda ta kashe sama da fam miliyan 400, wadda ta ɗauki ɗan wasa Aleɗander Isak daga Newcastle a matakin ɗan wasa mafi tsada a Ingila.
Wataƙila za a yi tata-ɓurza tsakanin ƙungiyoyin Premier League 20 da za su ƙalubalanci kofuna bana, har da na babbar gasar premier league ta Ingila wadda tuni aka buga wasanni uku.
Liɓerpool ce mai riƙe da kofin kuma na 20 jimilla da ta lashe a kakar da ta wuce, iri ɗaya da yawan wanda Manchester United take da shi a tarihin gasar premier ta ƙasar Ingila.
Ga jerin ƙungiyoyin da suka ci ribar kasuwancin sayen ƴan ƙwallo da waɗanda suka yi hasara a cikin ƙungiyoyin da suke buga gasar Premier League ta bana. Ƙungiyoyin da suka ci riba;
LIVERPOOL
Ƙungiyar ce kan gaba a yawan kashe kuɗi wajen sayen ƴan ƙwallo a bana, wadda karo biyu ta ɗauki ƴan wasa a matakin mafi tsada a kakar nan. Ta fara da sayen matashin ɗan wasa Florian Wirtz kan fam miliyan 115, sannan ta ɗauki Aleɗander Isak kan fam miliyan 125 ranar da za a rufe kasuwar.
Cikin ƴan ƙwallon da ta saye har da Jeremie Frimpong kan fam miliyan 30 da Milos Kerkez kan fam miliyan 40 sai kuma Hugo Eketike, ɗan Faransa, wanda ya koma ƙungiyar dafa Frankfurt. Haka kuma Liɓerpool ta sayer da Luis Diaz da Darwin Nunez da Jarell Ƙuansah daga ƙarshe ba ta samu damar sayen Marc Guehi daga Crystal Palace ba, bayan da Palace ɗin ta ce ba ta samu ɗaukar madadin Guehi ba.
ARSENAL
Arsenal ta fitar da maƙudan kuɗaɗe wajen sayen ƴan wasa da yawa, domin taimakawa Mikel Arteta a ƙoƙarin da yake na ganin ya lashe kofuna a bana, musamman Premier League, wadda rabonta da kofin kaka 22 kenan. Cikin ƴan wasan da ta ɗauka har da Viktor Gyokeres, wanda ya kawo matsalar rashin mai buga gurbin cin ƙwallaye, bayan da ke fama da jinya.
Haka kuma Arsenal ta sayi Eberechi Eze da Noni Madueke da Martin Zubimendi da Christian Norgaard da Cristhian Mosƙuera da kuma Piero Hincapie. Bugu da ƙari ƙungiyar ta London ta ɗauki mai tsaron raga Kepa Arrizabalaga, duk dai domin ta taka rawar gani a kakar nan, sannan Arteta ya ƙara lashe kofuna bayan FA Cup a kakarsa ta farko da kuma Community Shield.
NOTTINGHAM FOREST
Tuni ƙungiyar ta kori kocinta, Nuno Espirito Santo bayan rashin fahimtar juna da suke ci gaba da samu da daraktan ƙwallon ƙafa na ƙungiyar, Edu Gaspar, Forest ta shiga kasuwa ta yi cefanen ƴan wasa don ganin ta yi abin kirki a kakar nan.
Sau biyu a ƙungiyar tana sayen ɗan wasa a matakin mafi tsada a tarhinta, bayan sayen Dan Ndoye da kuma Omari Hutchinson. Sannan ta kuma kashe fam miliyan 30 kuɗin sayen James McAtee, sai kuma Douglas Luiz da ya koma buga Premier League daga Juɓentus ta kuma ɗauki Nicolo Saɓona.
A ranar da za a rufe kasuwar cinikin ƴan ƙwallo ƙungiyar ta sake ɗaukar aron Oleksandr Zinchenko ta sayi Dilane Bakwa, sannan ta kuma yi nasarar riƙe ɗan wasan tawagar Ingila, Morgan Gibbs-White, bayan da Tottenham ta yi ƙoƙarin sayen ɗan ƙwallon.
Sai dai duk da haka akwai ƙungiyoyin da za a iya cewa asara suka yi a wannan kakar idan aka kalli yan wasan da suka sayer da kuma waɗanda suka saye kafin a rufe kasuwar
NEWCASTLE UNITED
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Newcastle United ta sayi ɗan wasan Brentford, Yoane Wissa da ɗan ƙwallon Stuttgart, Nick Woltemade, wadda ta fara da ɗaukar ɗan wasan Nottingham Forest, Anthony Elanga.
Sai dai kuma ba za a manta da batun Aleɗander Isak ba, wanda ya dage sai da ya bar ƙungiyar, har da ƙin buga mata wasannin atisayen tunkarar kakar bana da wasa biyu da ta buga a Premier League ta bana.
Kuma rashin Isak ya sa tana shan wahala wajen cin ƙwallaye, hakan ya sa ta yi zawarcin madadinsa daga ciki har da Hugo Ekitike da ya zaɓi Liɓerpool da Benjamin Sesko da ya koma Manchester United har da Joao Pedro da ya zaɓi Chelsea sai kuma Jorgen Strand Larsen, wanda Woɓes ta ƙi sayer da shi.
ASTON VILLA
Ita ma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aston Villa tana fatan yin gogayya cikin ƴan shidan farko a Premier League a kakar nan, amma ta ci karo da cikas kan dokar kashe kuɗi daidai samu. Duk da haka ta sayer da matashi, Jacob Ramsey, wanda magoya baya ba su ji daɗi ba.
Sai dai ƙungiyar ta ɗauki Harɓey Elliott daga Liɓerpool da kuma ɗan wasan Manchester United, Jadon Sancho, amma dai Villa ba ta samu yin cinikin da zai bata damar yin abin kirki ba, kenan sai abin da ta gani.
BRENTFORD
Bayan da Brentford ta rasa kociyanta, Thomas Frank da ya koma Tottenham ta kuma sayer da ƴan ƙwallo uku da ya haɗa da Bryan Mbeumo ga Manchester United, yayin da Norgaard ya koma Arsenal da kuma Newcastle da ta sayi Wissa. Sai dai ta sayo Dango Outtara daga Bournemouth kan fam miliyan 42.5, amma dai tana da jan aiki bayan rashin fitattun ƴan ƙwallonta uku a kakar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp