Ma’aikatar aikin hajji da Umrah ta Kasar Saudiyya ta bayyana cewa, maniyyata sama da miliyan biyu ne, za su gudanar da aikin hajjin bana a Kasar Saudiyya.
Ministan ma’aikatar, Dakta Tawfiq Al-Rabiah ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar.
- Mataimakin Shugaban Kasar Gambia, Badara Joof, Ya Rasu A Indiya
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3, Sun Raunata Wasu A Katsina
Kafin dai bullar annobar Korona a kasar, adadin alhazan da suka gudanar da aikin hajji sun kai yawan miliyan uku a 2012, inda ya nuna cewa, wannan ne adadin da yafi yawa a tarihin kasa.
A 2013, biyo bayan fadada aikin Babban Masallacin Harami, ya sanya mahukuntan Kasar Saudiyya, sun rage yawan maniyyatan da za su je kasar don yin aikin na hajjin.