Cibiyar kasuwancin waje ta kasar Sin ta bayyana cewa, jimillar masu sayayya na ketare 224,372 daga kasashe da yankuna 219 ne suka halarci bikin baje kolin kayayyakin shige da fice na kasar Sin karo na 137 wanda aka fi sani da Canton Fair, ya zuwa karshen kashi na biyu na baje kolin a jiya Lahadi.
Kashi na biyu na baje kolin, wanda ke mai da hankali kan ingantattun kayayyakin gida, an fara shi ne a ranar Laraba tare da harabar baje kolin mai murabba’in mita 515,000. Wanda ya kunshi rumfuna 24,735 da masu baje kolin hajoji 10,313, adadin da ya karu da 273 bisa wanda ya gabata.
Kana, an tabbatar da fiye da kamfanoni 2,400 a wannan mataki a matsayin manyan masana’antun kasa masu ingantattun fasahohi, da masana’antu “kananan zakaru”, ko zakarun masana’antun kasa masu kera haja guda daya, kuma adadin ya karu da kamfanoni 100 idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.
Bikin baje kolin na wannan karo da ake gudanarwa a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin daga ranar 15 ga watan Afrilu zuwa ranar 5 ga watan Mayu, an shirya shi ne cikin matakai uku. Matakin farko ya mayar da hankali ne kan masana’antu masu ci gaba, na biyu a kan ingantattun kayayyakin gida, na uku kuma a kan kayayyakin dake sa kaimi ga inganta rayuwa. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp