A halin da ake ciki kuma, shugaban karamar hukumar Jibiya a jihar Katsina Hon. Bishir Sabiu Maitan ya bayyana cewa akwai fiye da mutane 150 da ke rike a hannun masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a karamar hukumar Jibiya.
Hon. Maitan ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake yi wa wakilan kafafen yada labarai bayani irin kokarin da gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Aminu Bello Masari akan ‘yan gudun hijira da ke makarantar ‘yan mata da GGSS Jibiya.
Shugaban ya kara da cewa kullum sai an kai hari a karamar hukumar Jibiya kuma kullum sai an dauki mutane da niyyar a biya kudin fansa kafin a sake su.
”Wannan al’amarin ya wuce duk inda ake tunanin sa, kusan yanzu na koma ba ni da wani aiki da wuce kula da ‘yan gudun hijira da kuma karbar rahotanni na kai hare-haren wuce gona da iri daga ‘yan bindiga, kullum maganar ke nan.”in ji shi.
Ya nunar da cewa yanzu haka akwai mutum 60 dukkansu ‘yan gari daya suna hannun ‘yan bindiga ana ta kokarin ganin yadda za a kubutar da su daga hannun masu garkuwa da mutane sai an ba da kudin fansa.
A cewarsa, “jami’an tsaro da kuma ita kanta gwamnati suna kokari sosai wajan ganin an kawo karshen wannan al’amari, amma fa idan an toshe can, sai can ya bude, Allah ya Kawo mana zaman lafiya,” in ji shi.
Shugaban karamar hukumar dai ya ce wannan adadin da ya ambata an dauke mutanen ne a cikin wata guda kacal, sannan ya kara da cewa a haka ma an sako wasu da iyalansu da suka biya kudin fansa.
Karamar Hukumar Jibiya dai tana cikin kananan hukumomin da ‘yan bindiga suka hana sakat, inda yanzu haka fiye da mutum 20,000 na gudun hijira, wasu a Nijeriya wasu kuma a jamhuriyar Nijer.
Haka kuma aikin ‘yan bindigar ya tilasta wa da yawa daga cikin magidanta tserewa su bar iyalan su, wasu kuma tuni suka riga mu gidan gaskiya, amma babar matsalar ita ce yadda wannan al’amari ya ki ci ya ki cinyewa.