Bukukuwan da aka gudanar na ranar abinci ta duniya kwanan nan sun isa su jawo hankalin gwamnati da al’ummar kasashen duniya a kan matsalar abinci da ake fuskanta a Nijeriya dama wasus assan duniya, wannan ya zama dole ne musamman ganin matsalar da aka fuskanta sakamakon annobar cutar Korona da kuma matsalar dumamar yanayi a duniya da kuma ambaliyar ruwar da aka fuskanta, ana wannan bikin ne a fadin duniya, ranar da ta yi daidai da ranar da aka kafa kungiyar nan ta Majalisar Dinkin Duniya ta UNFAO a shekarar 1945, bikin na da matukar muhimmanci don a wannan ranar ce al’ummar duniya ke haduwa don tattaunawa a kan matsalar da ake fuskanta ta karancin abinci ko kuma rashin abinci gaba daya a wasu sassan duniya.
Kamar dai yadda shirin samar da abinci a duniya (WFP) ya sanar, shekarar 2022 ta zamar wa al’ummar duniya wata fage na fuskantar matsaloli da suka shafi yanayin samar da abinci wadanda suka hadada rikice-rikice kamar abin da ke faruwa a yakin Rasha da Yukrain da lamarin dumamar yanayi da hauhawar farashin kayan masarufi haka nan kuma tayar da jijiyar wuya a tsakanin kasashe yana kara haifar da yanayin da noma zai gagara wanda hakan zai ka gai haifar da matsalolin abinci.
- Xi Ya Taya Murnar Shirya Bikin Liyafar Shekara-Shekara Ta Kwamitin Huldar Amurka Da Sin
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Tsohon Sakataren Gwamnatin Enugu Da Wasu
Wadannan matsalolin suntaimaka wajen haifar da rashin abinci irin wanda ba a taba gani irin shi ba atarihi.
Ra’ayin wannan jaridar si ne, an dade ana ta surutu a kan bukatar samar da yanayin da al’umma duniya za su samu damar samun ingantaccen abinci mai gina jiki.
A wannan mahangar muke jinjina da godiya da taken bikin na wannan shekarar wanda yake kamar haka, “Tafiya TareDa Kowa Da Kowa Don Samar Da Ingantaccen Abinci Mai Gina Jiki.”
Taken na wannan shekarar ya nuna muhimmancin hadin kai a tsakanin al’ummar duniya don karfafa tsarin samar da abinci a fadin duniya gaba daya.
Wannan ba tare da wata tantama ba suna cikin manyan matsalolin da al’ummar duniya ke fuskanta, cikin su kuma akwai talauci, rashin lafiya dalalacewar muhalli.
Don kawo karshen wannan matsalar a fadin duniya ara’ayinmu dole a samar da wani tsari da zai tafi tare da dukkan al’umma ba tare da nuna banbanci ba domin ai dukkan al’ummar duniya na da muhimmanci wajen samun nasarar wannan aikin.
A kan haka ne dole Gwamnati, Kamfanoni masu zaman kansu da Malaman jami’o’i da kungiyoyi masu zaman kansu da sauran daidaikun mutane su yi aiki tare da juna don samar da yanayin da kowa zai samu abinci cikin kwanciyar hankali ba tare da wata mastala ba.
Abin takaici ne a ra’ayinmu, duk da kokarin da ake yi na samar da ingantacciyar al’umma har yanzu mutane da dama a baya ba a tafiya da su, sun kasa cin gajiyar ci gaba da aka samu na kimiyya da fasaha a bangaren tattalin arziki da ta zamantakewa.
Abayyane lamarin yake, duniya nada abinci da al’ummar duniya za su iya ci ba tare da matsala ba amma kuma miliyoyin mutane a fadin duniya na kwana da yunwa wasu kuma ba su da ikon samun abinci mai gina jiki.
Muna kara jaddada cewa, annobar cutar Korona, Dumamar yanayi da mamayar kasar Yukrain da Rasha ta yi ya kawo cikas ga kokarin samar da ingantaccen abinci ga al’umma duniya da kuma shirin kawar da yunwa a fadin duniya.
Kididdiga ya nuna cewa, kasha 75 na mutanen da suke fuskantar matsalar abinci mutane ne da suka dogara da harkar noma a matsayin hanyar samun abincin su, su ne kuma suka fi dandanawa sakamakon da annobar da dan adam ya haifar wakansa yake kawowa, haka kuma sune suka fi fukantar rikice-rikicen da suka hada da na kabilanci da nuna banbanci a tsakanin maza da mata, wadannan mutanen na matukar bukatar tallafin kudade da kayan aikin noma na zamani don su samu hanyoyin samar da abinci ga al’ummarsu.
A daidai wannan rana ta abinci ta duniya, ya zama dole musamman ganin irin matsalolin da ake fuskanta a sassan duniya duniya su hada hannu don fuskantar matsalar ba tare da nuna banbanci ba, a kan haka ne dukkan bangarori na rayuwar al’umma suna da gudummawar da ya kamata su bayar don samar da abinci ingantacce da zai samar wa al’umma cikakkiyar lafiya.
Bincike ya nuna cewa, a shekafrar2021 misali, an kiyasta cewa kasha 29.3 na al’ummar duniya kusan mutum Biliyan 2.3 na fuskantar tsanani ko tsaka tsakanin matsalar abinci, haka kuma kashi 11.7 na al’umma duniya kusan mutum Biliyan 923.7 na fuskantar kololuwar tsananin matsalar abinci.
Haka kuma banbancin da ake samu a tsakanin jinsin mata da maza a kan yadda suke samun abinci yana kara fadadaa kullum.
A shekarar 2021, kasha 31.9 na mata a duniya na fuskantar matsanancin rashin abinci in aka kwatanta da kashi 27.6 na maza.
Rahoton ya kuma bayyana cewa a shekarar 2020, an kiyasta cewa kasha 22 na yara da basu gaza da shekara 5 suna fuskantar matsanancin rashin abinci, yayin da kashi 6.7 na yaran rashin abincin ya yi musu illa wasu kashi 5.7 na yaran kuma suna fuskantar cutar kiba saboda ciye-ciye marasa kangado.
Rahoton ya kuma kiyasata cewa, fiye da mutum miliyan 670 a fadin duniya za su fuskanci rashin abinci a cikin shekarar 2030 zuwa 2038, haka lamarin yake a shekarar 2015 a lokacin da aka kaddamar da shirin samar da abinci ga al’ummar duniya nan da shekarar 2030.
Mutum fiye da Miliyan 828 aka tabbatar sun fuskanci yunwa a shekarar 2021.
Bincike ya kuma nuna cewa daya daga cikin magidanta 8 a duniya na fuskantar cutar kiba a kusan dukkan bangarorin duniya ciki har da kasashe masu tasowa.
Ga Nijeriya kuwa harkokin ‘yan ta’adda yana kara tayar da hankalin al’umma game da shirin samar da abinci sai kuma ga gaggarumar ambaliyar ruwar da ta share filayen noma masu yawa.
Ra’ayinmu a nan shi ne na bukatar gwamnati ta kawo dauki ga manoman da suka yi asara a sassan Nijeriya. Dole a gaggauta kawar da al’amarin da muke tsoron aukuwarsa.