Gamayyar Ƙungiyoyin Matasan Arewa sun yaba wa Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, bisa bai wa Hon. Nasir Bala Ja’o’ji muƙami a Majalisar Zartaswa ta Babbar Kwalejin Ilimi da Fasaha ta Tarayya, Potiskum, da ke Jihar Yobe.
A wata wasiƙar taya murna da shugaban shiyyar ƙungiyar, Makama Dan Kaduna, ya sanya wa hannu bayan wani taro da suka gudanar a Kaduna, sun ce Hon. Ja’o’ji mutum ne mai kishin matasa da ƙoƙarin inganta rayuwarsu.
- Gwamna Radda Ya Gargadi Ƴan NYSC Kan Shiga Ƙungiyoyin Asiri
- ‘Yan Bindiga Na Kakaba Harajin Miliyoyin Naira Ga Mutanen Zamfara
Sun bayyana cewa, “Wannan naɗi da Sarkin Daura zai yi masa, ya ƙara tabbatar da binciken da muka gudanar wanda ya nuna cewa Hon. Ja’o’ji yana cikin shugabannin matasa 10 da suka fi fice da kwarjini a jihohin Arewa.”
Ƙungiyar ta kuma jinjina wa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, bisa ƙoƙarinsa wajen inganta rayuwar matasa.
Sun ce, “Nan ba da jimawa ba za mu fitar da sakamakon bincikenmu wanda ya gano 10 ciki har da Hon. Nasir Bala Ja’o’ji, da suka yi fice wajen tallafa wa matasa a Arewa. Za mu karrama su ɗaya bayan ɗaya.”
Sun ƙara da cewa, “Samun shugabannin matasa masu jajircewa a wannan yankin babbar albarka ce ga al’ummarmu.
“Hakan na nuna mana cewa akwai kyakkyawar makoma ta ci gaba a Arewa gaba ɗaya.”
Sannan sun bayyana cewa sun aike wa ƙungiyoyinsu a dukkanin jihohi 19 na Arewa goron gayyata domin naɗin sabbin muƙamai a Masarautar Daura.
“Za a gudanar da babban taron karramawa wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a nan kusa, domin naɗin sabbin muƙamai da Masarautar Daura za ta yi.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp