Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana a yau Alhamis cewa, Sin da Afirka suna daukar matakai na tinkarar sauyin yanayi, da sa kaimi ga samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba.
Yayin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ke ziyara a wasu kasashen Afirka, ya bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan ci gaban kasashen Afirka ba tare da gurbata muhalli ba, da yin kokari tare, wajen sa kaimi ga zamanintar da kasa, tare da kiyaye muhalli, da sada zumunta da juna.
- Da Gaske Ne Amurka Tana Kare ‘Yancin Fadin Albarkacin Baki?
- An Kashe ‘Yan Boko Haram Da Dama A Harin Da Suka Kai A Fadar Shugaban Kasar Chadi
Guo Jiakun ya kara da cewa, kasashen Afirka sun koyi fasahohin Sin a fannin dashen shingayen kare karfin iska na Sanbei, sun kaddamar da shirin dasa bishiyoyi na nahiyar Afirka, don daidaita matsalolin kwararar hamadar Sahara.
A fannin makamashi mai tsabta kuwa, kasar Sin ta aiwatar da daruruwan ayyuka a nahiyar Afirka. An shigar da fasahar noman ciyawar kasar Sin wato Juncao cikin nahiyar Afirka, aikin da ya zama kyakkyawan misali na hadin gwiwar Sin da Afirka kuma mai matukar amfani. Hakazalika kuma, ayyukan fasahohin samar da wutar lantarki ta karfin iska, da zafin kasa, da hasken rana, sun taimakawa kasashen Afirka wajen canja tsarin samar da makamashi.
Guo Jiakun ya kara da cewa, a nan gaba, za a aiwatar da ayyukan samar da makamashi mai tsabta guda 30 a nahiyar Afirka, da gina dakunan gwaji na hadin gwiwa guda 30, da yin hadin gwiwa a fannonin harba tauraron dan Adam, da binciken duniyar wata, da sararin samaniya da sauransu. Ya ce samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, ya zama muhimmin aikin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. (Zainab Zhang)