Sana’ar aikawa da kaya wato ‘Logistics’ a turance sana’a ce da ta kunshi aikawa da kaya daga wuri zuwa wani wuri daban ko kuma daga masana’anta zuwa mabukaci.
Wannan sana’a ce mai dinbin albarka musamman idan mai yin sana’ar na da cikakken ilimin da ake bukata mai yin sana’ar ya samu don idan babu wadatuwar ilimin mutum zai iya yin asarar jarinsa.
- Ancelotti Zai Zama Kociyan Tawagar Brazil A 2024
- Wang Yi Ya Bukaci Amurka Da Ta Dauki Kwararan Matakai Don Dawo Da Alakar Sin Da Amurka Kan Turbar Da Ta Dace   Â
Abubuwan da ake bukata yayin fara wannan sana’a su ne:
Bas/babbar mota ko kuma keken kaya. Wannan ya danganta da yanayin jarinka. Sari wato space, wannan shi ne ofis ko kuma wuri da za ka gudanar da sana’ar.
Kwamfuta
Wayar hannu wacce za ka iya yin sana’ar talla da kuma kiran kwastomominka da ita. Akwatin aike, wannan shi ne akwatin da ake saka kayan sakon a ciki, kayan aikin rubutu wato stationery.su ne kananan kayayyakin rubutun da ake amfani da su.
Wadannan su ne abubuwan da ake bukata yayin fara wannan sana’ar kuma sana’a ce wadda za ka iya farawa da jari kamar 500,000.
Yadda za ka fara wannan sana’ar
Wadannan su ne hanyoyin fara wannan sana’ar.
Da farko za ka zabi yanayin aikawa da sakon ka: Wannan muhimman abu ne.za ka zaba ko bus ne kake so ka fara da shi ko babbar mota ko kuma keken kaya ne kake da karfin saya. Idan ba ka da jari dayawa za ka iya farawa da zama wakili ko kuma ka fara da zama dan kwangila kafin ka fadada sana’ar.
Na biyu kuma shi ne tsara kasuwancinka: Ya kamata mai fara wannan sana’ar ya tsara abubuwa da dama kamar:
Bincike mai karfi akan sana’ar.zai iya bincike daga masu sana’ar takaitarwar zartarwa dabarun sana’a shirin kudi su waye tawagar sa da sauransu.
Na Uku Kuma Regista Da CAC,
Wato ka yi rajista da sunan sana’arka ko kuma kamfani mai iyaka wato Limited Liability Company ya fi saukin kudi.
Na hudu shi ne hannun jari
Jarin da kake da shi shi ma muhimmin abu ne da ya kamata mutum ya sani. Wannan sana’ar na da bukatar jari daga 500,000 zuwa sama.
Na biyar kuma shi ne; ka kirkirar intanet na sana’arka, wato logistics website.
Na shida kuma shi ne; Samun tsarin ofis wato office space. Wannan shi ne inda za ka rika gudanar da aiyukanka. Na bakwai kuma su ne; Ma’aikatan da za ka dauka, maaikatan da za ka dauka su zama wadanda za ka ba su horo a kan ayyukan da kake so su yi maka za ka iya farawa da kanka a matsayin direba saboda ka saba da hanyoyi da kuma kwastomominka.
Sai kuma na karshe shi ne ka tallata sana’arka za ka iya tallata sana’ar ka ta intanet kamar su WhatsApp, facebook, instagram da sauran su, kuma za ka iya tallata sana’ar ka ta abokanka.