Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a wannan shafi namu mai albarka. Yau za mu yi magana akan yadda ake sana’ar kamun kifi wato ‘Su’.
Sana’ar Su ita ce sana’ar kamun kifi da sauran halittun cikin ruwa. Sana’a ce mai dimbin albarka kuma sana’a ce dadaddiya wacce akan shiga ruwa ko dai kai tsaye a yi amfani da hannu ko kuma ta hanyar amfani da wani abu domin kama kifi a ciki ko a sayar. Wannan sana’a ta kamun kifi tana daga cikin dadaddun sana’o’in kasar Hausa.
- Wang Yi Da Qin Gang Sun Gana Da Ministar Harkokin Wajen Jamus
- Alhassan Ado Doguwa Ya Sake Lashe Zaben Dan Majalisar Wakilai A Kano
Mai yin wannan sana’a ana kiran shi da suna masunci. Ana gudanar da sana’ar kamun kifi a cikin kogi, tafki, korama, gulbi, injari da sauran wuraren wucewa da kuma taruwar ruwa.
Tasirin da sana’ar Su take da shi a kasar Hausa ya sanya su ma suna da sarkin ruwa. Sannan kuma suna bukukuwa irin nasu. Masunta kan jefa ‘ya’yansu a cikin ruwa su yi kwana da kwanaki a ciki ba tare da sun ciro su ba.
Kayan aiki
- Kugiya: Ana kafa ta a cikin ruwa a lankaya wani abu da kifi zai ci a jikinta, sai a baza ta a cikin wani yanki na ruwan da ake son kama kifi a ciki.
- Mali: Abu ne da ake yinsa da ita ce da raga ta zare. Ana tsoma shi cikin ruwa idan kifaye suka shiga ciki sai a fito da shi a kwashe.
- Kalli: Shi kuma raga ce ta zare ake kafewa a cikin ruwa, sai a ja ta zuwa wani gefen, idan kifaye suka taru a ciki sai a fito da su a adana.
- Birgi: Raga ce ta zare, wacce ake cin bakinta da dalma. shi kuma birgi watsa shi ake yi a cikin ruwa, sai dalmar ta shiga ciki baya iya fita, idan suka shiga ciki suka taru, sai a janye shi zuwa gabar ruwa a firfito da su a adana.
- Fatsa: Ita cards kugiya ce guda daya ko biyu ake daurawa a jikin sanda, sai a lankaya wani abincin da aka san kifi yana so, da zarar ya hadiyi wannan abincin, sai kukiyar nan ta makale masa a wuya, sai a fizgo da karfi a wullo shi wajen ruwa a kama.
- Dalla: ita ma raga ce ta zare, wacce ake rike gefe da gefenta, sai mutane su ratsa cikin ruwan suna ja. duk kifi da suka tokare shi to ba zai iya wucewa ba. Can zuwa wani lokacin sai su nannade ta da kifaye a ciki su fita da ita wajen ruwa sai su ciccire kifin.
- Koma: Ita koma jaka ce ta raga da ake yi wa katon baki. ridi biyu ake yin ta, ana rike kowacce daya kuma a hagu, idan aka shiga ruwa da ita sai a rika tafiya, can kuma sai a hade bakin a fitar waje.
- Gora: Gora hawa kanta ake yi ana iyo a cikin ruwa domin zuwa gurin da aka kafa mali, birgi ko makamantansu.
- Kwale-kwale: Abin sufuri ne na cikin ruwa. Da fatan wannan zai taimaka gun kamun kifi da sauran abubuwan ruwa. Allah ya ba da sa’a.