A wannan zamani da muke ciki, akwai wasu manyan sana’o’i bakwai da ake ganin sun fi taimakawa wajen saurin kawo wa mutane kudi a Nijeriya, wadannan kuwa su ne kamar haka:
Cinikin Gidaje
Sana’ar cinikin gidaje, na daya daga cikin manyan hanyoyin samun kudadade cikin sauki, musamman a wannan kasa da muke ciki. Domin kuwa, za ka iya sayen gida ka bayar da shi haya ko kuma sayen fili ka gina; daga bisani kuma ka sayar.
Wannan ne yasa wasu ke ganin babu abin da ya kai wannan sana’a tabbas da kuma samun kudaden shiga, sakamakon tsananin bukatar da ake da ita a bangaren matsuguni a daidai wannan lokaci, musamman ganin yadda gidajen haya ke matukar wahala; sakamakon rashin gina gidajen da ba a yi yanzu, saboda tsadar kayan gini da sauran makamantansu.
Noma
Babu shakka, bangaren harkokin noma a Nijeriya na ci gaba da habaka da kuma bunkasa. Wannan dalili ne yasa ake kara samun damammaki a wannan bangare da kuma samun bunkasuwar arziki.
Don haka, duk mai bukatar hanyoyin samun kudade masu yawan gaske; wajibi ne ya gaggauta rungumar wannan hanya ta noma a Nijeriya.
Kamfanin Makamashin Hasken Rana
Har ila yau, sanya hannun jari ko kafa kamfanin samar da makamashi ta hanyar hasken rana (Solar Farm), na daya daga cikin kasuwancin da yake matukar taimaka wa mutane a daidai wannan lokaci, wajen samun arziki ko kudade masu dimbin yawa a wannan zamani da muke ciki.
Kafa wannan kamfani ta hanyar amfani da makamashin hasken rana, na taimakawa wajen samar da hasken wutar lantarki tare da rarraba ta; ta hanyar sayar wa da masu bukata a samu kudi nan take.
Shakka babu, wannan hanya ce wadda a halin yanzu; musamman ganin yadda wutar lantarki ke matukar wahalar samuwa, mutane da dama sun raja’a wajen mayar da hankali; domin amfani da wannan makamashi, don samun wutar lantarki; wanda hakan ke matukar taimaka wa masu wannan sana’a wajen samun kudade masu yawan gaske.
Harkokin Cinikayya
Kasuwanci, wanda ya kunshi saye da sayar da abubuwa kamar man fetir, gwal ko zinare da kuma kayayyakin amfanin gona; na da matukar riba, amma na bukatar sani tare da fahimtar harkokin yadda ya kamata da kuma juriya.
Har ila yau, wannan kasuwanci na matukar garawa a wannan kasa tare da bayar da damar samun makudan kudade ga wadanda ke aiwatar da sana’ar.
Shi yasa duk wanda ka ga yana aiwatar da wannan kasuwanci na sayar da zinare ko sayar da mai, ba karamin attajiri ba ne, saboda sana’a ce mai matukar bukatar da isasshen jari.
Sayen Hannun Jari
A wannan gaba, sanya hannun jari; wata hanya ce da take da tabbas, sakamakon kulawa da gwamnati ta bai wa harkar tar da rage barazanar yiwuwar samun asara a cikinta. Sannan, ana kayyade adadin yawan abin da za a samu bayan tsawon wani lokaci da aka diba wa harkar.
Shi yasa, mutane da dama ke kutsawa cikin wannan kasuwa; ba tare da wani jin tsoro ba, ganin yadda harkar ke kawo kudi tare kuma da karancin yiwuwar tafka asara a cikinta.
‘Yan Nijeriya da dama, na aiwatar da wannan kasuwanci tare da samun makudan kudade lokaci bayan lokaci a fadin wannan kasa da muke ciki a saukake.
Kudaden Da Kwararru Ke Sarrafawa
A nan, wata kasuwa ce da wasu kwararru ke sarrafa nau’o’in kudade daban-daban, dangane da yadda kasuwar hada-hadar kudaden ke juyawa. Sannan, wannan kasuwanci; baya bukatar mai aiwatar da shi ya rika zurfafa bincike a cikinsa.
Manajojin asusun, su ne ke yin wannan bincike tare da tafiyar maka da hada-hadar kasuwancin, kai kana zaune abinka. Kazalika, abin da kawai kai ake bukata a wajenka shi ne; zuba wannan hannun jari a cikin kudaden da ake hada-hadarsu tare da duba ribar da kake samu ta yau da kullum.
Ajiyar Kudi Zuwa Wani Kayyadadden Lokaci
wannan na daya daga cikin hanyoyi masu sauki na samun kudi a huce da sunan kasuwanci. Abin da kawai ake nema a nan shi ne, mai sha’awar wannan kasuwanci; ya zuba jarinsa a kamfani, sannan ba zai waige shi ba; har sai bayan wa’adin lokacin da aka diba ya cika.
Babu shakka, wannan kasuwanci na da matukar riba; sannan kuma babu asara ko kadan a cikinsa, domin kuwa za a iya samun ribar da ba a taba tsammani ba; kamar yadda tsarin kasuwancin yake.