Kwanan nan, kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, wato jam’iyya mai mulki ta kasar Sin, ya gudanar da cikakken zaman taro, inda ya yi nazari tare da amincewa da shawarwari game da shirin raya kasar Sin na shekaru biyar masu zuwa (2026-2030). Sanarwar da aka fitar bayan taron ta bayyana cewa, ci gaban kasar Sin zai fuskanci samun damammaki da kalubale cikin shekaru biyar masu zuwa. Duk da haka, muhimmin yanayin da ke tallafawa bunkasar tattalin arzikin kasar Sin bai canza ba. Wannan bayani ya nuna kwarin gwiwa da shugabannin kasar Sin suke da shi wajen fuskantar kalubale da ka iya bullowa a nan gaba.
To, daga ina wannan kwarin gwiwa ya fito? Da farko dai, ya samo asali ne daga tabbacin dabarun raya kasar Sin.
Tun da dadewa, manufofin kasar Sin suna mai da hankali kan dabaru na dogon lokaci, maimakon kula da moriyar gajeren lokaci kawai. Kasar Sin ta ba da fifiko ga tsare-tsare na matsakaici da na dogon lokaci don jagorantar ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma, kuma ta tsara tare da aiwatar da tsare-tsaren raya kasa na shekaru biyar-biyar guda 14 daya-bayan-daya.
Shirin raya kasa da kasar Sin ta gabatar a wannan karon ya hada da ci gaba da sa kaimi ga samun bunkasa mai inganci, da kara samun dogaro da kai a fannin kimiyya da fasaha, da kyautata rayuwar jama’a, da tabbatar da tsaron kasa, da kuma cimma matsayin yawan GDPn kan mutum na matakin kasashe masu matsakaicin ci gaban tattalin arziki nan da shekarar 2035. A bayyane yake, idan aka yi la’akari da yadda kasar Sin take ci gaba da samun bunkasa mai inganci, samun nasarar wadannan manufofi ba zai zame mata abu mai wuya ba.
Na biyu, wannan kwarin gwiwa ya samo asali ne daga yadda kasar Sin ta nuna jajircewa wajen fuskantar dimbin kalubale daban-daban.
A cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sakamakon matakan takunkumi da kasar Amurka ta dauka kan kamfanonin fasahohin zamani na kasar Sin, kasar Sin ta kara saurin yin kirkire-kirkire a matsayin mai zaman kanta, wanda ya haifar da karuwar sabbin nasarori a fannonin da suka hada da fasahohin kere-kere, da na’urar mutum-mutumi, har ma ta zarce sauran kasashe a wasu muhimman fasahohin zamani.
Sa’an nan, dangane da takunkumin da wasu kasashen yammacin duniya suka kakaba mata, kasar Sin ta yi kokarin inganta karfin jure wahalhalu da tabbatar da kiyaye bangaren masana’antu da samar da kayayyaki, tare da rage tasirin matsalolin da kan taso daga waje yadda ya kamata. Wadannan ingantattun hanyoyin mayar da martani ga matsin lamba daga ketare sun nuna cikakkiyar juriyar tattalin arzikin kasar Sin.
Bisa wannan kwarin gwiwa, kasar Sin ta shirya wajen fuskantar kowane irin kalubale, da kiyaye saurin bunkasar tattalin arziki da kwanciyar hankalin zaman al’umma a cikin dogon lokaci, da kuma sa kaimi ga aikinta na zamanantar da al’umma. (Bello Wang)