A yau Litinin ne aka fitar da sanarwar hadin gwiwa ta bayan taron tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka a birnin Geneva na Switzerland.
Cikakkiyar Sanarwar:
Gwamnatin kasar Sin da gwamnatin Amurka sun amince da muhimmancin alakar raya tattalin arziki da kawancen cinikayya tsakanin kasashen biyu da ma duniya baki daya. Sun gamsu da muhimmancin wanzar da hakan, cikin tsawon lokaci, da moriyar tattalin arziki da cinikayya tsakaninsu. Sun kuma yi duba game da tattaunawar da suka gudanar a baya bayan nan, kana sun gamsu cewa, ci gaba da tattaunawa nan gaba zai taimaka wajen warware abubuwan da suke jan hankalinsu ta fuskar alakar tattalin arziki da cinikayya, da ci gaba bisa ruhin budewa juna kofa, da kara tattaunawa da hadin gwiwa da martaba juna.
Sassan biyu sun amince da aiwatar da wadannan matakai daga 14 ga watan nan na Mayu na 2025.
Amurka za ta sauya matsaya kan adadin harajin fito da ta ayyana kan hajojin dake shiga kasar daga Sin, ciki har da kayayyakin da suka fito daga yankin kusamman na Hong Kong da yankin musamman na Macau, wadanda ke karkashin dokar shugaban kasa mai lamba 14257 ta ranar 2 ga watan Afirilun 2025, ta hanyar jingine karin kaso 24 bisa dari na harajin a wa’adin farko na kwanaki 90, yayin da kuma sauran karin kaso 10 bisa dari da aka ayyana dorawa za su gudana bisa tanadin dokar, kana za ta kawar da karin harajin fito kan kayayyakin Sin karkashin dokar shugaban kasa mai lamba 14259 ta ranar 8 ga watan Afirilun 2025 da ta 14266 ta ranar 9 ga watan na Afirilun 2025.
Kasar Sin za ta sauya matsaya kan adadin harajin fito da ta ayyana kan hajojin dake shiga kasar daga Amurka karkashin sanarwar sashen haraji na hukumar kwastam mai lambar 4 ta 2025, ta hanyar dage karin kaso 24 bisa dari a wa’adin farko na kwanaki 90, tare da wanzar da karin kaso 10 bisa dari kan kayayyakin, da jingine sauyin harajin fiton karkashin tanajin sashen haraji na hukumar kwastam mai lambar 5 na 2025, da sanarwar sashen haraji na hukumar kwastam mai lamba 6 na 2025. Kazalika Sin za ta aiwatar da dukkanin matakai na hukuma wajen dage sauran matakan ramuwar gayya da ba na karin haraji ba da ta ayyana kan Amurka tun daga ranar 2 ga watan Afirilun 2025. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp