Sanata mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta Kudu, Sanata Shehu Buba Umar ya ƙarya labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa Majalisar dattawa ta amince da ƙirƙiro sabbin jihohi guda 12, ya misalta labarin da cewa bai da tushe balle makama.
da yake ganawa da ƴan jarida a Bauchi ranar Asabar da ta gabata, Buba ya fayyace cewa, a halin da ake ciki dai majalisar ta kafa kwamitocin jin ra’ayin jama’a daga sassa daban-daban har guda shida na ƙasar nan dangane da kwaskwarima ga kundin tsarin mulki na 1999 tare da neman ƙirƙiro sabbin jihohi da ƙananan hukumomi.
Ya tabbatar da cewar a halin yanzu majalisar dattawa ko karɓar rahoton kwamitocin jin ra’ayoyin jama’a ba ta yi ba, balle ta zauna ta tantance ta duba wuraren da suka dace a amince da samar da sabbin jihohi ko ƙananan hukumomi a cikinsu.
- Gwamna Ademola Adeleke Ya Ƙaryata Jita-Jitar Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC
- Majalisar Dattawa Za Ta Yi Zama Na Musamman Don Karrama Buhari
LEADERSHIP Hausa ta rawaito cewa, tun kafin gudanar da taron jin ra’ayin jama’a a shiyyoyi ƙasar nan, majalisar dattawa ta amshi buƙatun neman ƙirƙiro sabbin jihohi guda 46, ciki har da buƙatar neman samar da Jihar Katagum daga cikin Jihar Bauchi. Sai dai, a rahoton da aka yada, babu sunan Katagum a cikin wadanda aka ce majalisar ta amince da su, lamarin da ya sanya jama’a da dama daga yankin suka fara ƙorafi da nuna matuƙar damuwa.
Jihohin da aka ce an amince da su sun hada da a yankin Kudu Maso Yamma, Ijebu (daga cikin Jihar Ogun) da Ibadan (daga cikin Jihar Oyo), Kudu Maso Gabas, Anim (daga yankunan jihohin Anambra da Imo ) da kuma sabuwar Jihar Adada (daga cikin Jihar Inugu), Kudu Maso Kudu kuwa, Toru-Ibe (daga sassan Jihohin Ondo, Edo, da ɗelta) da kuma Obolo (daga Akwa Ibom), Arewa Maso Gabas, Saɓanna (daga Jihar Borno) da Amana (daga Jihar Adamawa), Arewa Maso Yamma, Tiga (daga cikin Jihar Kano) da Gurara (daga kudancin Jihar Kaduna) da kuma yankin Arewa ta Tsakiya, Okura (daga Jihar Kogi State) da kuma Apa (daga cikin Jihar Benuwe).
Sai dai tuni masu sanatoci da dama, kamar Sanata Shehu Buba, da Sanata Abdul Ahmad Ningi da ke wakiltar Bauchi ta tsakiya suka ƙaryata labarin da cewa babu gaskiya a cikinsa tare da neman jama’a da su yi watsi da shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp