Sanata Henry Seriake Dickson da ke wakiltar Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawa ya bukaci ‘yan Nijeriya da su tashi tsaye su yaki matsalar sayen kuri’a da buga sakamakon zabe na bogi.
Dickson ya bayyana hakan ne a tattanawa da manema labarai yana cewar masu ruwa da tsaki da ‘yan Nijeriya bakidaya suna da hakkin gyara abubuwan maras kyau da ke faruwa a kasar nan.
- Hadimin Gwamnan Yobe Ya Fice Daga APC Ya Koma Jam’iyyar ADC
- Ba Ni Da Niyyar Barin APC Zuwa Wata Jam’iyyar — Gwamna Zulum
Tsohon Gwamnan na Bayelsa ya ce gurbatattun abubuwan da ke gudana a karkashin jagorancin masu hali da ‘yan siyasa masu fada aji lamari ne da zai tarwatsa tsarin siyasar kasar nan.
Sanatan na jam’iyyar PDP ya bayyana fatara da rashin sani a matsayin kashin bayan da gurbatattun ‘yan siyasa ke amfani wajen samun kuri’a ta hanyar amfani da kudi da sauran abubuwa.
Ya ce wannan matsalar ta jefa ‘yan Nijeriya a cikin kunci da mayar da kasa baya domin mutanen da ba su cancanta ba ke rike da mukamai wadanda babu nauyin da suke saukewa bayan samun nasara.
“Na yi Allah- wadai da amfani da madafun iko da tsara sakamakon zabe kafin zabe ta hanyar amfani da karfin mulki da hukumomin gwamnati.”
“Wajibi ne Hukumar Zabe ta samu hanyoyin magance wadannan matsalolin a wajen jefa kuri’a maimakon neman hakki a bangaren shari’a wanda daga karshe kotu za ta sanya wasu dubaru ta kori kara mai kyau ta fashin zabe.” Ya bayyana.
Ya ce irin wannan matsalar na samar da mutanen da ba su ko iya cin zabe a cikin dangin su ko al’ummar su amma sune ke tinkahon lashe zabe.
A cewarsa a matsayinsa na dan majalisar dattawa suna kokarin gabatar da dokokin da za su shawo kan wadannan matsalolin, ya ce sun san hukumar zabe ba za ta iya kula da abubuwan da jami’an tsaro ke yi a yayin zabe ba.
“Shine dalilin da yasa ake canza sheka zuwa jam’iyya mai mulki domin samun damar amfani da madafun ikon cin zabe ta kowace irin hanya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp