Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar mazaɓar Kogi ta Tsakiya, ta bayyana cewa ta jinkirta komawarta majalisa ne saboda shawarwarin lauyoyi da kuma bin dokoki, duk da cewa kotu ta soke dakatarwar da aka yi mata.
A wata hira da ta yi da gidan talabijin na AIT, Sanata Natasha ta ce tana jiran takardar hukuncin kotu kafin ta ɗauki matakin komawa majalisar.
- Tinubu Ba Zai Yarda Hayaniyar Siyasar 2027 Ta Ɗauke Masa Hankali Ba – Ministan Yaɗa Labarai
- NiMet Ta Yi Hasashen Cikin Watan Yulin 2025 Za A Tabka Ambaliyar Ruwan Sama A Jihohin Nijeriya 19
“Ina da cikakken yaƙini game da shari’a, kuma ba zan fasa ba,” in ji ta, tana nuna ƙwarin gwiwarta ga tsarin shari’a.
Ko da yake kotu ta ce dakatarwar da aka yi mata ta yi yawa kuma ba bisa ƙa’ida aka yi ta ba.
Wani lauya daga Majalisar Dattawa, Paul Daudu (SAN), ya bayyana cewa hukuncin bai ƙunshi umarnin tilasta majalisar ta dawo da ita ba.
Wannan ya janyo tambayoyi kan ko za ta iya komawa nan take.
A lokacin da aka tambaye ta me take yi a lokacin da aka dakatar da ita, Sanata Natasha ta ce ba ta tsaya ba, har yanzu tana gudanar da ayyuka tare da wakiltar mutanenta.
“Na kasance ina aiki a duk lokacin. Na ci gaba da aiki kuma ina shirin gabatar da wasu dokoki a kan ma’adanai. Ba zan iya miƙa su ga wani ba,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa duk da cewa ba ta halartar zaman majalisa, ta ci gaba da yin ayyukan ci gaba ga mutanenta.
“Fitar da ni daga majalisa ba kawai ni aka daƙile ba, an hana muryar Kogi ta Tsakiya fitowa fili,” in ji ta.
“Majalisar Dattawa ta hana mata da yara ‘yan Nijeriya samjn wakilci. Yanzu muna da Sanata mata guda uku kacal, alhali a baya muna da takwas.”
LEADERSHIP ta ruwaito cewa sanarwar dawowarta da aka shirya yi a ranar Talata ta tayar da hankula a majalisar, inda aka tsaurara tsaro kuma aka kawo motocin jami’an tsaro da dama.
Shige da fice daga harabar majalisar ya kasance a ƙarƙashin kulawar jami’an tsaro, inda ake bincikar motoci kafin ba su iznin shiga.
Ko da yake ba ta koma majalisar ba tukuna, Sanata Natasha ta jaddada cewa za ta ci gaba da yin aikinta.
“Ina da niyyar ci gaba da wakiltar Kogi ta Tsakiya da Nijeriya gaba ɗaya,” in ji ta.
“Ko na je majalisa ko ban je ba, zan ci gaba da sauke nauyin da ke kaina.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp