Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya, Uba Sani ya Karyata labarin da ke yawo a kafar sada zumunta ta zamani cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan kudurin kirkiro sabuwar jihar Zazzau wanda kuma aka yi zargin cewa, Sanata Sulaiman Abdu Kwari ne ya dauki nauyin wannan kudurin.
Malam Uba Sani wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a karkashin inuwar Jam’iyyar APC mai mulki, ya karyata rahoton ne a cikin sanarwar da ya fitar da kansa a jihar Kaduna.
Ya ce, ta ya ya mutane ke son tarwatsa jihar su, bayan jihar na fuskantar kalubalen rashin tsaro, domin kawai Sanata Uba na kara samun goyon bayan al’ummar jihar a takararsa ta neman gwamna a 2023.
Ya ce, a yanzu Majalisar Dattawa na kan hutu ne kuma babu maganar wani kuduri mai kama da hakan a gaban Majalisar ta Dattawa kamar yadda kafafen na yada labarai suka yi Ikirarin.
Uba ya ce,”Mun mayar da hankali wajen tunkarar fara yin gangamin yakin neman zabe a watan Satumbar 2022 don cin nasara a zaben 2023 a saboda haka, babu wani yarfe na siyasa da wasu ke kitsa wa da zai karkatar da hankalin mu”.