Daya daga cikin Shugabannin ‘yan ta’adda, Alhaji Shanono da mayakansa su 17 sun gamu da ajalinsu bayan da sojojin saman Nijeriya suka kai musu hari a jihar Kaduna a ranar Talata.
An kashe Alhaji Shanono da mayakansa ne yayin wata tattaunawa da mayakansa a wani taro da suka yi a Ukambo, wani kauye mai tazarar kilomita 131 daga Kaduna, a wani harin da jirgin yakin rundunar Air Component na ‘Operation Whirl Punch’ ya kai.
Wani babban hafsan sojin sama ya shaidawa LEADERSHIP cewa sama da bindigu 30 da babura 20 ne aka lalata yayin da Mutane 26 da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su suka tsere bayan harin da jiragen suka kai musu.
Ya ce, “Sakamakon hare-haren da jirgin NAF ya Kai, ya nuna cewa an kawar da ‘yan ta’adda da dama tare da lalata matsugunan su. Daya daga cikin irin wannan hare-haren da rundunar sojin ta kai a ranar 9 ga watan Agusta, 2022, ya yi sanadin kawar da wani fitaccen shugaban ‘yan ta’adda da ke barna a jihar Kaduna.
“Hakika, bayan samun bayanan sirri a ranar 9 ga Watan Agustan 2022 cewa wani Shahararren shugaban ‘yan bindiga, Alhaji Shanono, ya shirya ganawa da mayakansa a Ukambo, wani kauye mai tazarar kilomita 131 daga Kaduna, sai rundunar Air Component ta Operation Whirl Punch ta aike da jirgin Yaki don ganin bayan ‘yan ta’addan.”