Mataimakin Shugaban masu tsawartar wa a Majalisar Dattawan Nijeriya kuma wakilin mazabar Neja ta Arewa, Aliyu Sabi Abdullahi, ya yi watsi da sakamakon zaben fidda gwani na Jam’iyyar APC da aka gudanar a mazabarsa. Â
Sabi ya zargi gwamnan jihar Alh. Abubakar Sani Bello, da yin nune da kuma karya ka’idojin da Jam’iyyar APC ta gindaya na gudanar da zabe da kuma dokar zabe ta 2022.
Cikin takardarsa ta koke da ya gabatar wa da shugaban kwamitin da ya gudanar da zaben a mazabarsa, Sabi ya yi kira ga kwamitin da ya soke zaben wanda ya yi zargin cewa an tabka magudi da danne hakkin jama’a.