Tsofaffin mataimaka na musamman ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wadanda suka tsaya takara a jam’iyyar APC na neman kujerar gwamna da majalisar dattawa da na majalisar wakilai a Jihar Kano dukkan su sun sha kaye a zaben fitar da gwani.
Sun dai hada da Sha’aban Sharada, wanda shi ne tsohon mataimaki na musam-man ga shugaban kasa kan watsa labarai, wanda a halin yanzu haka shi ne shuga-ban kwamitin majalisar wakilai kan fasahar tsaron kasa da tsohon mataimaki na musamman kan kafafen yada labarai na zamani, Bashir Ahmad da kuma tsohon mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan bunkasa zamantakewa, Ismaeel Ahmed duk sun sha kaye a zaben fitar da gwani da ya gabata a Jihar Kano.
Sun dai sha kayen ne a hannun ‘yan takarar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mara wa baya.
Shi dai Sha’aban ya tsaya takarar gwamna ne a karkashin jam’iyyar, yayin da Bashir ya nemi samun tikitin takarar dan majalisa na mazanar Albasu/Gaya/Ajingi, sai kuma Ismaeel da ya nemi tikitin takarar dan majalisar dattawa na Kano ta tsakiya.
Ismaeel ya bayyana janyewar takararsa mintina kadan kafin gudanar da zaben fitar da gwani. Amma shi Sha’aban da kuma Bashir an gudanar da zaben fitar da gwanin da su wadanda suka sha kaye.
Bayanai dai sun nuna cewa, Ismaeel ya janye takararsa ne bayan da gwamna ya tabbatar masa da cewa Abdulsalam Abdulkarim Zaura zai bai wa tikitin takara.
Sha’aban dai ya samu kuri’u 30, yayin da abokin karawarsa mataimakin gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna wanda ya lashe zaben ya samu kuri’u 2,289.
Bashir dai ya samu kuri’a 16, yayin da abokin karawarsa da ya lashe zaben, Abdul-lahi Mahmoud Gaya ya samu kuri’u 109.
Masu sharhi kan zaben Kano sun bayyana cewa sakamakon zaben fitar da gwani na takarar gwamnan bai zo da mamaki ba, saboda Sha’aban yana takun-saka da gwamna da kuma shugabannin jam’iyyar APC na jihar tun a shekarar 2021.
Shi kuma Bashir a tunaninsa zai iya samun tikitin takarar dan majalisar wakilai ci-kin ruwan sanyi tun da dai ya kasance yaro ne ga fadar shugaban kasa kamar dai abokinsa Sha’aban, amma bai yi nasara ba.
Majiyar ta tabbatar da cewa, lokacin da Bashir ya bayyana wa shugaban kasa a niyarsa ta tsayawa takara ya amince da bukatarsa kamar dai sauran ‘yan takara da suka bayyana masa aniyarsu. Amma kuma hakan bai hana shi shan kaye ba.
Shi dai Bashir ya zargi shugabannin jam’iyyar a jihar da yin masa magudi a zaben, inda ya yi zargin an yi amfani da ‘yan daba a kansa da kuma magoya bayansa wajen tursasa musu barin wurin zaben.
Masu saka ido a zaben sun bayyana cewa bayan rashin gogewa a siyasar mazaba, babban abin da ya sa mutanen Buhari suka sha kaye shi ne, shugaban kasa bai nuna sha’awa a cikin takararsu ba.