A ranar Laraba ne Sanatoci suka nuna rashin jin dadinsu kan yadda hukumar kula da kadarorin Nijeriya (AMCON) ke gudanar da ayyukanta.
‘Yan majalisar sun yi hasashen cewa, Hukumar ta yi asarar Naira biliyan N146 a cikin watanni 12.
- Kwamitin Majalisar Dattawa Ya Nemi A Karawa Ma’aikatar Yaɗa Labarai Kudi Kan Kasafin 2024
- Kamfanin NNPCL Ya Zuba Naira Tiriliyan N4.5 Cikin Watanni 10 A Asusun Gwamnati – Kyari
An bayyana asarar kudaden ne a lokacin da Babban Daraktan AMCON, Ahmed Kuru da tawagarsa suka bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin banki, inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi karkashin jagorancin Sanata Adetokunbo Abiru.
Baya ga shugaban kwamitin, mambobin kwamitin sun hada da Sanata Sani Musa, Jimoh Ibrahim, Adamu Aliero, Ifeanyi Ubah, da dai sauransu.
‘Yan majalisar sun tabbatar da cewa, AMCON ya ta tafka asara akai-akai a cikin shekaru 13 da suka gabata kuma sun fada kai tsaye cewa, kamfanin baida wani amfani yanzu.