Tun bayan ƙaddamar da majalisar dattawa ta 10 a ranar 13 ga Yunin 2023, majalisar na shan suka daga wasu ‘yan Nijeriya waɗanda suke ganin ta zama ‘yar amshin shatan a ɓangaren fadar shugaban ƙasa.
Masana harkokin siyasa sun yi iƙirarin cewa sabbin sanatocin yanzu suna yin aiki ne ba don cika ƙa’idoji ba, suna amincewa da ƙudirorin da ɓangaren zartarwa ya gabatar ko wasu manyan hukumomi suka yanke hukunci, maimakon shiga cikin tsarin samar da dokoki da wakilci na gaskiya da kuma gudanar da bincike da tsarin mulki ya ɗora wa majalisa.
- Sanata Shehu Buba Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Da Rigakafin Shanu A Bauchi
- Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Masanan sun bayyana damuwarsu kan cewa akwai rashin ‘yancin kai na gaske da kuma sake yin nazari mai zurfi ta yadda majalisar take amincewa da sakamako da aka riga aka yanke.
Wasu ‘yan Nijeriya sun bayyana rashin jin daɗinsu kan cewa sama da sanatoci 40 ba sa yawan halartar taron majalisa da zaman kwamitoci ko kuma ba da gudunmawa a muhawara ake fafatawa a zauren majalisar dattawa.
Hazalika, masana harkokin siyasan sun cewa yawancin ‘yan majalisar dattawan zai yi wuya su halarci zaman majalisar tun daga ranar Talata zuwa Alhamis a kowane mako. Sun nuna matuƙar damuwa kan wannan lamari, wanda ko ma sun zo suna kasancewa masu ɗumama kujera ne kawai ba tare da gabatar da wani ƙudiri ba duk da adadin kuɗaɗen da suke karba a matsayin alawu da albashi da sauran fa’idodi da ake ba su.
Yawancin ‘yan Nijeriya sun nuna damuwa game da yadda majalisar dattawa ta 10 ke gudanar da harkokin majalisa, suna cewa ‘yan majalisar sun gaza bayar da muhimman ayyukan da aka ɗora musu na binciken ɓangaren zartarwa don kare ‘yan Nijeriya.
Ana zargin majalisa dattawa ta 10 da ƙin tilasta wa gwamnatin tarayya wurin magance tarin ƙalubale da ke fuskantar ‘yan Nijeriya, ciki har da tsadar rayuwa, talauci, yunwa, yawan rashin aikin yi da rashin tsaro, da sauran su.
Rahotanni su bayyana cewa akwai tsofaffin gwamnonin 13 da ke majalisar dattawa ta 10 a halin yanzu, wanda suka haɗa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Aliyu Wammako (Sakkwato), Abdulaziz Yari (Zamfara), Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato) da Adams Oshiomhole (Edo).
Sauran sun haɗa da Ibrahim Hassan Dankwambo (Gombe), Abubakar Bello (Neja), Orji Uzor Kalu (Abiya), Seriake Dickson (Bayelsa), Adamu Aliero (Kebbi), Danjuma Goje (Gombe), Gbenga Daniel (Ogun) da Simon Lalong (Filato).
Masana sun ce daga cikin tsofaffin gwamnonin 13 da ke majalisar, Akpabio, Aliero, Dickson, Oshiomhole, Kalu, Lalong, Daniel, da Goje su ne suke taka rawar gani sosai a lokacin tattaunawan zaman majalisa.
Akwai rahotannin da ke cewa Yari, Dankwambo, Bello, Tambuwal da Wamakko ba sa yawan halartar tarurrukan majalisa ko kuma su shigo cikin muhawara idan sun bayyana. Duk da haka, akwai rahotannin da ke cewa wasu ƙananan ƙudirori ne suka gabatar a zauren majalisar.
Haka zalika, sanatoci irinsu Sahabi Yau, mai wakiltar Zamfara ta Arewa da Eze Kenneth Emeka, mai wakiltar Ebonyi ta tsakiya da Okechukwu Ezea, mai wakiltar Inugu ta Arewa da Anthony Siyako Yaro, mai wakiltar Gombe ta Kudu da Mustapha Khabeeb, mai wakiltar Jigawa ta Kudu da Rufai Hanga, mai wakiltar Kano ta tsakiyar da Binos Dauda Yaroe, mai wakiltar Adamawa ta Kudu da Benson Friday Konbowei, mai wakiltar Bayelsa ta tsakiya da Eteng Jonah Williams, mai wakiltar Kuros Ribas ta tsakiya da Adegbonmire Ayodele, mai wakiltar Ondo ta tsakiyar dukkansu ba su gabatar da wani ƙudiri ba a zauren majalisar dattawa ba har izuwa yanzu.
Haka kuma, akwai sanatoci irinsu Amos Yohanna, mai wakiltar Adamawa ta Arewa da Samaila Kaila, mai wakiltar Bauchi ta Arewa da Ani Okorie, mai wakiltar Ebonyi ta Kudu da Kelɓin Chizoba, mai wakiltar Inugu ta Gabas da Jiya Ndalikali, mai wakiltar, Neja ta Kudu da Onyesoh Allwell, mai wakiltar Ribas ta Gabas da Haruna Manu, mai wakiltar Taraba ta Tsakiya da Napoleon Bali, mai wakiltar Filato ta Kudu da Fadeyi Olubiyi, mai wakiltar Osun ta tsakiya da Shuaibu Isa Lau, mai wakiltar Taraba ta Arewa na daga cikin rukunin sanatocin da ba sa magana a zauren majalisar dattawa.
Sauran su ne Fasuyi Cyril Oluwole, mai wakiltar Ekiti ta Arewa da Osita Ngwu, mai wakiltar Inugu ta Yamma da Onyewuchi Francis, mai wakiltar Imo ta Gabas da Ahmed Madori, mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso Gabas da Lawal Adamu Usman, mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya da Musa Garba, mai wakiltar Kebbi ta Kudu da Sadiƙ Suleiman Umar, mai wakiltar Kwara ta Arewa da Olajide Ipinsagba, mai wakiltar Ondo ta Arewa da Yunus Akintunde, mai wakiltar Oyo ta Tsakiya da Abdulfatai Buhari, mai wakiltar Oyo ta Arewa da Mpigi Barinda, mai wakiltar Ribas ta Gabas da Babangida Husseini Uba, mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso Yamma da Bassey Etim, mai wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Gabas da Emmanuel Udende, mai wakiltar Benuwai ta Arewa maso Gabas da Godiya Akwashiki, mai wakiltar Nasarawa ta Arewa da Ikra Aliyu Bilbis, mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya da Oyewumi Kamorudeen Olarere, mai wakiltar Osun ta Yamma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp