Jadon Sancho ya kammala komawa tsohuwar kungiyarsata Borrusia Dortmund inda zai saka riga mai lamba 10.
Dan wasan mai shekaru 23 ya bar Manchester United ya koma tsohuwar kungiyarsa ta Bundesliga a matsayin aro.
- 2027: Atiku, Kwankwaso Da Obi Na Shirin Kafa Babbar Jam’iyyar Adawa – Pat Utomi
- Ogun: Kotun Koli Ta Dakatar Da Karar Korar Abiodun
An bayyana komawar Sancho a hukumance a yammacin yau Alhamis a shafin sada zumunta na Borrusia Dortmund.
Komawa kasar Jamus zai taimaka wa matashin dan wasan na kasar Ingila ya cigaba da taka leda, domin tun watan Agusta rabonsa da buga wasa a United.
United ta sayi Sancho daga Dortmund a lokacin bazara a shekarar 2021 a kan kudi fam miliyan 73.
Kwantiragin Sancho zai kare a shekarar 2026, tare da United amma tana da zabin tsawaita kwantiraginsa tsawon shekara guda.