Tsawon lokaci a wannan Kasa, za a ga cewa da daman jama’a na da kaikayi, miki da tarin raunuka iri daban daban a zukatansu, game da irin salon yadda Kotunan Zabe ke tafikad da shari’unsu na zabe daga lokaci zuwa lokaci. Na’am, sanannen abu ne ga duk dan Kasa cewa, bayan kammala babban zabe na du-gari ne, kundin tsarin mulkin Kasar ya shar’anta samar da irin wadancan Kotuna, da zimmar duk wani dan takara ko wata jam’iyya da ke da korafi, zai je ya shigar da irin nasa ko ke ne a gabansu.
Na’am, duk jam’iyyar da ba ta sami nasara a irin wadancan Kotuna ba, labudda za ta gamu da rashin jindadi ainun, za kuma ta iya kausasa harshe tare da yin suka, a ilmance ne ko a jahilce, ga irin wadancan Kotuna. Sai dai, ga al’amarin irin wadannan Kotunan zabe a yau a Najeriya, akwai caccaka gami da kalubalen da ake antayowa musu, wanda suke fitowa daga bakunan masana shari’a, ba daga bakin wata jam’iyyar siyasa ko wani dan jam’iyya ba. Ke nan, akwai bukatar nazartar lamarin da idon basira.
- Al’adun Kasar Sin Na Da Tushen Neman Zaman Lafiya Tun Lokacin Da
- CISA: Masana’antun Sarrafa Karfe Na Tafiya Cikin Yanayi Mai Karko Tsakanin Watan Janairu Zuwa Na Agusta
Duba da irin yadda lamarin Kotunan Zaben ya jima da tabarbarewa a idon da daman “yan Najeriya, yayinda ake fuskantar zabukan Shekarar 2003, masana harkar shari’a irinsu tsohon shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya, NBA, DCJ Okocha SAN, ba a bar su a baya ba, wajen jan-hankalin Kotuna, na su dawo cikin haiyacinsu, su kawar da son zuciyar da yai musu katutu, tare da bukatar yin hukuncin shari’un zaben bisa adalci da gaskiya, tare da kaucewa son zuciyar da masu mulki ka iya zuwa musu da ita, don ganin an tabbatar da nasarar shari’un da za su gudanar ga jam’iyyar gwamnati. Bugu da kari, Okocha SAN, ya fadi cewa, akwai alamun gwamnatin taraiya na da burin sake amfani da Kotunan Shari’a wajen durkusar da wannan Jamhuriyar Siyasa ta Hudu (4th Republic) da muke ciki, tamkar irin yadda ya afku a zaben 12 ga Watan Yuni na Shekarar 1993 (June 12,1993).
(Tell September 16, 2002)
Shari’ar Nasiru Gawuna Da Dahiru Oska
Duba da irin abinda ya faru a zaben kujerun kananan hukumomi na Shekarar 2007 a Kano, tsakanin tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, lokacin da yake jam’iyyar ANPP, da kuma Dahiru Abdu Oska na jam’iyyar PDP a wannan jamhuriyar siyasa ta hudu, a gaban wata Kotun Saurarar Korafin Zabe a Kano, sai wasu ke fassara lamarin da cewa, ashe ma ba tun yau ne ba Gawunan ke fakewa da alfarmar irin wadancan Kotuna, tare da turmushe hakkin abokanan shari’arsa.
Waccan shari’a ta Gawuna da Oska, an yi ta ne sa’adda Oska ke ganin shi ne halastaccen mutumin da ya lashe zaben karamar hukumar Nassarawa, jihar Kano, ba Gawuna ba. Amma saboda wani irin walagigi da Kotunan Zaben ke da, sai bayan da Gawuna ya kammala zangon mulkinsa bisa kujerar ta Ciyaman, wanda ya fara daga Shekarar 2007 zuwa 2011, sannan ne kuma wai Kotun ta tabbatar da gaskiyar cin zabe ga Dahiru Oska. Shin, mene ne amfanin irin wannan gaskiyar da aka tabbatarwa da Oska?. Ta ina ne Oska zai amfana da gaskiyar da Kotu ta ba shi a kurataccen lokaci, alhali ba hawa kujerar zai yi ba? Don Allah mene ne hikimar Kotu a wannan hukunci?.
Dadin dadawa, sai waccan Kotun zabe ta ba da umarnin a biya Dahiru Oska dukkanin hakkokinsa na jumlar kudaden da ba a ba shi ba, a matsayinsa na halastaccen wanda ya ci zabe a dokance!. Ba ma ta fuskar siyasa ko shari’a ba, hatta ta fuskar tattalin arzikin Kasa, an cutar da lalitar karamar hukumar, tun da mene ne hikimar mutum biyu su amshe kudin Ciyaman biyu, kuma a karamar hukuma guda? Sannan, Kotu ba ta nemi Nasiru Yusuf Gawuna da ya maido da ko sisi ba zuwa cikin asusun karamar hukumar ta Nassarawa!!!.
Cikin rubutun da ya gabata, an dan gabatar da irin yadda gwamnatin tsohon shugaban Kasa Obasanjo ke amfani da Kotunan na Zabe ta haramtacciyar hanya. Inda shugaban ke amfani da wasu hanyoyi ko tarkuna iri hudu (4), wajen kassara kashin bayan abokanan hamaiyarsa ta siyasa ciki da waje, “yan jam’iyyar adawa da ma “yan jam’iyyarsa. Yakan yi amfani ne da hukumar zabe, INEC, farko, idan mutum ya tsallake wannan tarko, sai kuma ya yi amfani da hukumar yaki da cin-hanci, EFCC. Bugu da kari, tarko na uku shi ne, sai ya kafa wani kwamitin boge, da zai sa a dankarawa mutum farar takarda “white paper”. Hanya ta karshe da Obasanjo ke kassara abokanan rigimarsa ta siyasa da ita shi ne ta hanyar hada-baki da Kotuna, a karbewa mutum zabe, ko kuma a ce wai mutum bai ma cancanci ya tsaya zaben ba.
Lamarin yin dari-dari ko sanyin-gwiwa ga Kotunan Zaben da waninsu, wani al’amari ne da yai geza har zuwa wannan lokaci da muke ciki, wato har zuwa lokacin wannan zabe na Shekarar 2023. Kasa da Sati biyu da ya gabata, tsohon Ciyaman na Kwamitin Shari’a da Hakkin Dan’adam na zauren Majalisar Dattijai ta Kasa, Umar Dahiru, ke tabbatar da irin rashin kwarin gwiwa da al’umar Nijeriya ke da, game da batun Kotuna a wannan Kasa.
Sanata Dahiru ya yi wancan ikirari ne lokacin da ya je bikin kaddamar da wani littafi da aka kira da “When Justice Sleeps : Burning Issues and Crises in Administration of Justice in Nigeria”, a takaice, littafin na yin nuni da irin yadda lamura suka tabarbare ne a bangaren shari’a na wannan Kasa. Sai Sanatan ya kada baki ya ce;
“… Nigerians habe lost hope in the country’s judicial system…”
“… Babu shakka “yan Nijeriya sun rasa kwarin gwiwa game da irin tsarin da ake gudanar da shari’a cikin wannan Kasa…”.
Sannan, Sanata Dahiru ya danganta waccan tabarbarewa da bangaren na shari’a ya yi da son zuciya cikin rigar addini da kabilanci da kuma bangarenci, uwa uba kuma da sabgar cin-hanci da rashawa da ta yi wa jama’a katutu. Saboda haka ne ma Sanatan ke cewa, yanzu ne da ma lokacin da ake tsaka da bukatar fitowar littafi irin wannan. Wato rubuce-rubuce da za su mayar da hankali zuwa ga ankarar da jama’ar Kasa game da yanayi na kaico da bangaren na shari’a ke ninkaya cikinsa a yau. In ji Sanatan, yanzu an kai kadamin da idan mutum ya ce a zo a tafi Kotu, wasu ke fassara hakan da a je ne a zalunci mutum.
Matthew Okeke, a matsayinsa na mawallafin wancan littafi, shi ma ya tofa nasa albarkacin baki, inda yake yin nuni da cewa, hakika bangaren shari’a na wannan Kasa ya jima da samun kansa cikin yanayin tabarbarewa. Yanzu haka bangaren ba ya yin aiki irin yadda ya kamata ya yi. Bangaren shari’ar a yau, ba ya biyawa mutane cikakkun bukatunsu, sai hakan ya bayu zuwa ga rashin samun gamsuwa da jama’ar ke yi game da bangaren.
Cikin jaridar Banguard ta sha-shida ga Watan Satumbar wannan Shekara, 2023, an yi bayanin cewa, jama’ar Kasa sun yi matukar kaduwa duba da irin tumbudin hukunce-hukuncen da Kotunan Saurarar Korafe-korafen Zabuka suka yi. Kamar yadda jaridar ke fadi, zuwa wannan rana ta 16 ga Satumba, an rushe zabukan Sanatoci 7, kuma an rushe kujerun zabukan “yan majalisar taraiya 23.
Daga abinda jama’a ke korafi akai game da waccan marka-marka ta rushe kujerun wadancan zaba6bu shi ne, daga cikin rusassun kujerun, sai a ga cewa, jam’iyyar APC ta rasa kujeru 5 ne; jam’iyyar PDP kuwa ta rasa kujeru 14 ne; jam’iyyar LP kuwa kujeru 6 ne ta rasa; jam’iyyar NNPP ta rasa kujeru 2 ne. Sannan kuma, idan da za a dubi kujerun da jam’iyyun suka marabta da su ko a ce suka samu, sai ya kasance jam’iyyar APC ta sami nasarar dafe kujeru 7 ne; jam’iyyar PDP ta sami kujeru 5; jam’iyyar LP ta sami kujeru 2, ita kuwa jam’iyyar APGA ta tsira ne da kujera 1 ne tal.
Daga abinda ya sanya mutane wasu-wasi shi ne, idan aka dubi lissafin sama, sai a ga cewa, jam’iyyar gwamnatin taraiya, idan an zo batun wace jam’iyya ce ta fi kowace jam’iyya tafka asarar kujerun da aka tube a duk fadin Kasa?, tun da batun asara ne, sai a ga cewa, wata jam’iyya ce daban ba jam’iyyar shugaban Kasa ba ta fi yin asarar. Sannan, idan kuma an zo lissafa wace jam’iyya ce ta fi kowace jam’iyya samun tagomashin nasara a duk fadin Kasa a Kotu?, tun da samu ne, sai kuma a ga cewa jam’iyyar shugaban Kasa ce ta fi kowacce nasara.
Duk da wancan lissafi na 16 ga Satumba, da za a kara dubawa, sai a ga jam’iyyar gwamnatin ta ci gaba ne da girbar nasara sama da sauran jam’iyyun bakidaya. Misali, a wancan lissafin, ai za ga cewa, jam’iyyar NNPP ta rasa kujerar “yan majalisa 2 ne. Amma zuwa 27 ga Satumbar, sai a ga NNPPn ta kara rasa kujera guda, alhali kuma jam’iyyar shugaban Kasa ta APC ta fa ci gaba ne da kara karbar kujeru abinta. Ko ma mene ne dalili, jama’ar Kasa na kokawa da irin wannan lissafi na dokin rano!!!.
Taho-mu-gama A Hukuncin Kotunan Zabe
Wasu mutane daga jam’iyyun adawa da ma waninsu, na yin kuka da irin karo da juna da ake samu cikin hukunce-hukuncen da Kotunan Zabe ke gudanarwa. Korafin da wasu ke yi a nan shi ne, a kan fitar da hukunci iri daban daban a kan mas’ala iri guda. Babban abin takaicin shi ne, a kan sami nau’in wani hukunci ma da za a ga tuni Kotun Koli ta fadi yadda za a yi idan aka sami irin wannan matsala, amma abin haushi, sai a iske wata Kotun Zabe ta ki amfani da wancan hukunci na Kotun Koli, ta lalubi wani hukunci na daban ta yi. Alhali sanin kowa ne cewa, hukuncin Kotun Koli a wannan Kasa na sama ne da kowane irin hukunci da wata Kotu za ta tsuguna ta yanke.
Masu wancan korafi sun gabatar da hujjar cewa, sau da yawa sai a ga wasu Kotuna sun shiga wata sabgar da a dokance kwata-kwata ba su da wani hurumi a ciki. Misali, kamar abinda ya shafi rikicin fitar da wani dan takara a wata jam’iyyar siyasa. A fili yake cewa dambarwar fitar da dan takara, ko abinda ya shafi shiga cikin jam’iyya iri kaza, hurumi ne da babu wata Kotu da take da hurumin shiga sabgar, amma sai a ga wasu Kotunan sun tsunduma kansu ciki. Jam’iyya ce kadai kacokan da ke da ikon cewa, wannan ne dan takarata ba wancan ba.
Irin wancan hurumi na jam’iyya ita kadai game da batun fitar da dan takara daga jam’iyya, akwai wani hukunci da Kotun Koli ta yi, mai lamba SC/CB/501/2023, wanda ta tabbatar da cewa, ka da ma wata Kotu ta ce za ta yi wani hukunci game da batun fitar da wani dan takara daga wata jam’iyyar siyasa, yin hakan tamkar wani shisshigi da bai da goyon bayan wata Doka. Ta ci gaba da tabbatar da ikon hakan a hannun jam’iyyun na siyasa.
Dole ne irin wancan katsalandan da ake zargin wasu Kotunan Zabe da yi, ya rika alamta kokwanton adalci da aiki bisa doron gaskiya ga wasu Kotunan, duk da cewa ba duka ne aka taru aka zama daya ba. Ma’ana, za a iya samun wasu jagororin Kotunan da duk wuya ko rintsi, za su tsayu ne inda Doka ta umarce su.