Tun bayan da Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya karbi rantsuwar kama aiki, ya yi alkawarin bincikar tsohon gwamnan Kano kuma shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan zargin almundahana, karbar cin hancin dala da kuma zargin da ake masa na kasafta wasu wurare mallakar al’ummar Jihar Kano ne.
Wannan tasa kwana kadan da karbar ranatsuwar Gwamna Abba ya fara dirar wa wasu gine-gine a filin idi da kuma kantunan da aka gina a filin sukuwa, sannan kuma ta dirar wa ginin tsohon otal din Daula.
- Sabon Shirin Auren Zawarawan Kano A Sikeli
- Za A Fara Amfani Da Sabon Layin Jirgin Ƙasa Na Dakon Kaya Daga Legas Zuwa Kano A Watan Gobe
Daukar wannan mataki ya sa ‘yan kasuwar filin wadanda aka rushe wa kantunansu suka garzaya gaban kotu, inda ita kuma kotun ta dakatar da gwamnatin Kano daga ci gaba da aiwatar da wannan rusau tare da tarar naira biliyon uku. Wannan mataki na kotu ne ya dakatar da yunkurin Gwamnatin Abba na ci gaba da rushe ire-iren wadanna wurare.
Tun daga lokacin da Jam’iyyar NNPP mai mulkin Kano ta kai bantenta a kotun koli, sai labari ya sauya, inda aka fara karkade tsoffin zarge-zargen da ake yi wa tsohon Gwamna Ganuje, wanda suka hada da karbar dala, watandar filayen mallakar gwamnatin Jihar Kano da wasu laifuka da ake zargin shugaban Jam’iyyar APC na kasa ya aikata.
Gwamnatin Kano ta himmatu wajen cika alkawarin da ta yi wa Kanawa na bincikar Ganduje, wanda tun da farko an ji cewa dansa ya gurfanar da mahaifiyarsa, Farfesa Hafsat Ganduje a gaban kotu kan zargin wawure kudaden wasu ‘yan kwankgila. Wannan tasa cikin kunshin zargin da Gwamnatin Abba ke yi wa Ganduje har da batun iyalansa, wanda aka gwamnatin Kano ta kaddamar da kwamtin bincike guda biyu a kansa.
A lokacin kaddamar da kwamitin binciken, Gwamna Abba ya bukaci su tabbatar an hukunta wanda duk aka samu da laifi. A cikin wani jawabi da mai magana da yawun Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya bayyana cewa, gwamnan ya jadddada aniyarsa na bincikar al’mundahanar dukiyar al’ummar Kano, wanda hakan na cikin kokarinsa na zakulowa tare da hukunta duk wanda ke da hannu cikin yunkurin tayar da tarzoma a Jihar Knao.
Kwamitin farko na karkashin Mai Shari’a Zuwaira Yusuf, wadda aka dora wa alhakin bincikar rikicin siyasar tare da batan mutane daga shekara ta 2015 zuwa 2023, sai kuma kwamiti na biyu da ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Faruk Lawan wanda aka dora wa alhakin bincikar almundahanar kadarorin al’umma.
Kamar yadda aka tabbatar alkalan na da kyakkyawan tarihin ingancin aiki da kuma gaskiya da adalci, wanda hakan a dukkan zaton da ake za a iya samun adalci cikin aikin biciken. An dai bai wa kwamitocin binciken wa’adin watanni uku domin gabatar da rahotonsu.
Gabanin kaddamar da wadannan kwamitocin bincike, an ta samun musayar zafafan kalamai tsakanin Ganduje da kuma Gwamna Abba, wanda tun da farko Ganduje ya zargi Gwamnatin Kano da kulla kitimurmurar haddasa zanga-zangar bukatar sai ya sauka daga shugabancin jam’iyyar APC, haka kuma ya zargi Gwamnatin Kano da kulla wani shirin korarsa daga mazabarsa, wanda ya ce duk wannan ba zai sa ya jijjiga ba wajen ci gaban ayyukan alhairin da yake yi.
 Anasa bangaren, Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabri Yusuf ya musanta wannan zargi ta bakin mai magnaa da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa wanda ya ce, kamata ya yi Ganduje ya shagala da abin kunyar da ya tafka tare da shirya fuskantar binciken da ake masa, ba wai ya shagala da kazafin gazawar gwamnati mai ci a yanzu ba. Sanusi ya shaida cewa Gwamnatin Abba ba za ta bari batun dala ya lalace ba, saboda haka suka bukaci hukumar EFCC da ta fito da sakamakon binciken faifan dala da suka gudanar domin jama’a su san halin da ake ciki.
A wata sabuwa kuma, dan Ganduje wanda tun da farko ya fara gurfanar da mahaifiyarsa gaban kotu kan korafin wasu kudade, an hange shi ya ziyarci ofishin shugaban hukumar karbar korafe-korafe ta Jihar Kano. Ya tabbatar wa da shugaban hukuma Muhuyi Magaji Rimin Gado cewa zai taimaka wa hukumar wajen ba da shaida domin samun nasarar bincikar mahaifin nasa.
A zaman kotun da aka a ranar Litinin ta makon jiya, wanda aka gudanar a kotu mai lamba ta uku da ke zamanta a sakatariyar Audu Bako a Kano, alkalin kotun ya bukaci dukkan bangarorin guda biyu su shirya gabatar da bayanansu a zaman da za a yi nan ga ba kadan.
Ganduje na cikin tsaka mai wuya, kasancewar ana ta gudanar da zanga-zangar neman sauke shi daga mukamin shugaban jam’iyyar APC na kasa, yayin da a hannu guda kuma yake fuskanta matukar adawar cikin gida, inda wasu ke zargin faduwar jam’iyyar a kotun koli da hadin bakisa domin biyan wata bukata, sai dai kuma yadda Gwmanatin Kano ke yin duk mai yiwuwa domin ganin an gurfanar da Ganduje tare da wasu daga cikin iyalansa saboda su fuskanta hukuncin abin da suka aikata.
A yanzu haka an fara ganin wata sabuwar hula wadda ke dauke da kalar ja da samfurin hular Tinubu, wadda hakan ke nuna alama cewa kila ana kan shirye-shiryen sauya shekar Jam’iyya NNPP zuwa APC, wannan kuma na cike da manyan kalubale, musamman tsoron da Kwankwasa ke yi na komawa APC karkashin Ganduje, idan haka ta faru kenan har yanzu Kwankwaso da Kwankwasiyya na karkashin Ganduje.
Wani hange da ake yi wa Shugaba Tinubu cewar sai dai ya zabi guda cikin wadannan manyan ‘yan siyasar Kano, ma’ana ko dai ya hakura da Gnaduje ya karbi Kwankwaso, ko kuma ya bar Kwankwaso ya kama Ganduje, wanda kuma yin hakan shi ma a gareshi babban kalubale ne ga zaben 2027.