Tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya gudanar da zaman fada na farko a yau Litinin a gidan Nasarawa, inda ya sauka tun bayan komawarsa Kano a ranar Asabar. Sarkin ya fito da cikakkiyan kayan sarauta, Sarki Aminu ya karbi magoya bayansa da wasu hakimai, wanda hakan ke nuni da ci gaba da da’awarsa na karagar mulkin Kano duk da cewa majalisar jihar Kano ta yi dokar sauke shi da sauran Sarakunan Gaya da Bichi da Karaye da kuma Rano.
Lamarin ya haifar da wani yanayi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin Kano, inda mutane biyu ke da’awar halaccinsu a matsayin sarki. Muhammad Sanusi II, wanda gwamnatin jihar Kano ta dawo da shi, ya ci gaba da gudanar da tarukan karramawa a babbar fadar Kano da ke kofar kudu, kuma tuni wasu manyan hakimai har sun kai gaisuwar ban girma.
- Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Gina Rukunin Gidaje 500 A Kano
- Matsayar Ƙungiyar Sarakunan Arewa A Tsaya Kan Umarnin Kotu Kan Rikicin Sarki 2 A Kano
Rundunar ‘yan sandan jihar ta sha alwashin bin umarnin da kotu ta bayar na hana a dawo da Sanusi har sai an warware kullin da ya dabaibaye nadi da cire tsohon Sarkin. Haka zalika Aminu Ado shi ma na ci gaba da zaman fada a gidan Nasarawa a karkashin tsauraran matakan tsaro.
Hankula sun fara tashi a jiya Lahadi yayin da magoya bayan Aminu Sarki Aminu Ado suka gudanar da zanga-zanga, lamarin da ya kai ga daukar tsauraran matakan tsaro. Daga bisani kwamishinan ‘yansandan jihar Kano yayi gargadi kan yiwuwar kai hare-hare a wasu muhimman wurare a jihar.