Sarki Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa za a sake sanya ranar naɗa ‘Wamban Kano’ a matsayin Hakimin Bichi a Masarautar Kano.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Bichi na ɗaya daga cikin masarautun da gwamnatin jihar Kano ta dakatar watannin baya tare da mayar da masarautar karkashin Masarautar Kano.
- Xi Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Zababben Shugaban Ghana
- Kotu Za Ta Saurari Ƙalubalantar Ikonta Da Emefiele Ke Yi Kan Shari’arsa
Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar tawagar shugabanni masu rike mukamai na masarautar da Malaman addini a fadarsa da ke Kano, ranar Laraba.
Idan dai ba a manta ba, a ranar Juma’ar da ta gabata ne, jami’an tsaro suka tare fadar Sarkin Kano tare da hana Sarki Sanusi II tafiya don gudanar da bikin nada Munir Sunusi a matsayin Hakimin Bichi.
Tawagar wacce shugaban karamar hukumar Bichi, Hamza Sule ya jagoranta, ta je fadar ne domin jaddada mubaya’ar al’ummar Bichi ga masarautar.