Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, ya amince da naɗa Alhaji Sanusi Ado Bayero, Wamban Kano na yanzu, a matsayin sabon Galadiman Kano, wani babban muƙami na sarautar Kano.
An amince da wannan naɗi ne a zaman majalisar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a ranar Laraba 16 ga Afrilu, 2025. A cewar wata takarda da babban jami’in gudanarwa Awaisu Abbas Sanusi ya rattabawa hannu, za a gudanar da bikin naɗin ne a ranar Juma’a 2 ga Mayu, 2025 da karfe 9:00 na safe a fadar Sarkin da ke gidan Nassarawa.
- Sanusi II Ya Naɗa Sabon Galadiman Kano
- Ka Cire Sarkin Kano Bayero Daga Fadar Nasarawa – Gwamnatin Kano Ga Tinubu
Takardar da aka aika zuwa ga Alhaji Sanusi Ado Bayero ta isar da umarnin Sarkin tare da taya shi murna saboda wannan ƙarin girma. An kuma buƙaci ya sanar da ’yan’uwa, da abokai da masoya domin su halarci bikin don nuna farin ciki da wannan naɗi.
Alhaji Sanusi Ado Bayero, wanda ya kasance fitaccen dan gidan sarauta, ana sa ran zai kawo kwarewarsa ta gwamnati da al’adu don ci gaba da inganta tsarin mulkin masarautar.
Wannan naɗi ya zama wani babban mataki a cikin mulkin Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda ke ci gaba da kiyaye al’adun masarautar tare da haɗa kan al’umma.
Sai dai kuma a cikin wannan wata ne Sarkin Kano na 16 Sanusi Lamido Sanusi II, ya fara naɗa Alhaji Mannir Sanusi (Hakimin Bichi) a wannan muƙami bayan rasuwar tsohon Galadima.
Za a iya cewa dai yanzu bayan Sarakuna biyu Kano na da Galadima biyu da aka naɗa a wata guda sakamakon Sarkuna biyun dake da’awar zama halattaccen Sarki, duk da dai Sarki Sanusi Lamido II shi yake gidan Rumfa yayin da Sarki Aminu ke gida masauƙin baƙi da na Nassarawa da ya mayar da shi sabuwar fadarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp