Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Kasa (NSCIA), Sa’ad Abubakar III, ya umarci al’ummar Musulmi da su fara duban jinjirin watan Zul-Hijja daga ranar Laraba.
Sarkin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a Sokoto a yau Talata, mai dauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin bada shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi da ke Sokoto.
- Hare-Haren ‘Yan Bindiga Ya Tilasta Yara 3,000 Daina Zuwa Makaranta A Katsina
- Kotu Ta Yi Wa Wadanda Suka Kashe Wani Zabiya Daurin Rai Da Rai A Malawi
“Ana sanar da al’ummar musulmi cewa ranar Laraba 29 ga watan Yuni daidai da 29 ga watan Zul-Qidah 1443AH ita ce ranar da za a duba jinjirin watan Zul-Hijjah 1443AH.
“Saboda haka, an bukaci Musulmai da su fara duban jinjirin watan a ranar Laraba kuma su kai rahoto ga gunduma ko kauye mafi kusa don tuntubar Sarkin Musulmi,” “in ji sanarwar.
Sarkin Musulmi, ya roki Allah da ya taimaki al’ummar Musulmi wajen gudanar da ayyukansu na addini.
Zul-Hijja shi ne wata na 12 kuma na karshe a cikin kalandar Musulunci da ake gudanar da aikin Hajji a cikinsa, kuma ake yin idin layya.