Sarkin Musulmai, Sa’ad Mohammad Abubakar II, ya yi kira ga ‘yan Njeriya da su daina tsine wa shugabanni ko zaginsu, inda ya horesu da su bari Allah ya yi maganinsu a lokacin da ya so.
Ya nusar da cewa, babu wani abu mai kyau ko rashinsa da ke dauwama har abada, sai ya karfafi ‘yan Nijeriya da su dukufa wajen ci gaba da yi wa shugabanni da kasar Nijeriya addu’a domin samun zuwa ga tudun mun tsira.
Sarkin Musulmi ya kuma yi amfani da wannan damar wajen tunatar da shugabanni da su tuna da ranar tashin alkiyama, inda Allah Madaukakin Sarki zai titse su don su yi bayani filla-filla kan yadda suka gudanar da jagorancin jama’a, kuma, su sani babu wani mahalukin da zai karesu a gaban mahaliccinsu.
Bugu da kari, ya gargadi shugabannin addini da su daina wawantar da hankulan magoya bayansu bisa wata ra’ayi ko muradinsu na kashin kai, inda ya yi bayanin cewa kaso 90 cikin 100 na mutanen da suke sauraron shugabannin addini a masallatai da cocina su na aminta da ababen da suke gaya musu a matsayin hakan ne mafita a garesu.
Ya yi bayanin cewa, Allah ne kawai zai ceci kowani mutum. Ya hori jama’a da su ji tsoron Allah su sani akwai ranar sakamako ga komai, sannan, ya ce, komai bai fi karfin Allah ba, don haka a koma gareshi da neman mafita.
Sultan ya yi wannan fadakarwar ne a yayin taron da aka shirya ga malaman da fastoci kan sauyin yanayi da rigingimu a arewacin Nijeriya, wanda reshen kungiyar daidaito da fahimtar juna ta Kaduna ta shirya da hadin gwiwar ‘International Alert’, a ranar Litinin.
“Ku yi imani da bautar da kuke wa Allah ku bar masa komai, ba wai ga waninsa ba. Ka da ku bari wasu su shashantar da ku daga wannan. Abubuwa da dama suna faruwa a kasar nan, mun yi imani kuma dole ne mu koma ga Allah. Mu zurfafa yin addu’o’i ga kasar nan a dukkanin masallatai. Ban ambaci cocina ba ne saboda shugaban CAN yana nan a nan wajen, ina da yakinin zai ce wani abu irin hakan.”
Ya ce, arewacin Nijeriya na fuskantar matsaloli da daman gaske ba kawai ga sauyin yanayi ba, har ma da talauci, matsalar tsaro, dukka a arewaci da aka santa a da baya da zaman lafiya da ci gaba sosai.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban kungiyar Kiristoci na kasa (CAN), Dakta D.C. Okoh, ya ce, tabbas akwai sauyin yanayi a arewa, sai ya misalta da rikicin da ke damun jama’a kuma akwai bukatar daukan matakan shawo kan hakan.