Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana jimaminsa kan labarin rasuwar tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi a ƙasar Ingila.
A cikin wata sanarwar ta’aziyya da Sakataren Jama’atu Nasril Islam (JNI), Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ya fitar, Sultan ya yi addu’ar Allah ya karɓi ayyukan alheri da Buhari ya yi, ya kuma ya gafarta masa kura-kuransa.
“Marigayi shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari an san shi da rayuwa mai sauƙi, kuma ya kasance mai jajircewa wajen tsayawa kan gaskiya”
“Sarkin musulmi ya yaba da irin gudunmawar da ya bayar wajen hidimatawa al’umma tsawon shekaru masu yawa, muna addu’ar Allah ya karɓi ayyukan alheri da ya yi, ya yafe masa kura-kuransa, ya jikansa ya kuma gafarta masa,” in ji sanarwar.
Sarkin ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ta musamman ga iyalan marigayin da gwamnatin Nijeriya da kuma al’ummar ƙasa baki ɗaya, musamman jama’ar jihar Katsina.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp