Mai Martaba Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya, ya bayyana takaicinsa kan matsalar wutar lantarki da ake yawan samu ta hanyar sakaci ma’aikatan JEDC.
Sarkin ya nuna damuwarsa ne a lokacin da ya gayyaci jami’an hukumar ta JED zuwa fadarsa, kan rashin wutar lantarki a garin Ningi, inda ya bayyana cewa Ningi ta cancanci samun wutar lantarki mai inganci saboda yawanta mutane da ayyukan kasuwanci a yankin da ma tarihin da take da shi.
- Me Ke Shirin Faruwa Tsakanin Sarkin Katsina Da Gwamnan Jihar?
- Zargin Tube Sarkin Musulmi: Kallo Ya Koma Sakkwato
A nasa martanin, Manajan tashar JED na Ningi, Sani Ya’u Sallau, ya bayyana cewa sun damu da yadda ake satar wayoyi da sauran na’urorin lantarki a garin na Ningi.
Sallau ya tabbatar wa sarkin cewa su na iya bakin ƙoƙarin ganin sun shawo kan wanna matsalar.