Allah Ya yi wa Sarkin Tikau a Jihar Yobe, Alhaji Muhammadu Abubakar Ibn Grema ya rasuwa.
Wata majiya daga iyalinsa ce ta tabbatar da rasuwar Sarkin da yammacin ranar Juma’a, bayan ya sha fama da doguwar jinya a Asibitin Kwararru na Potiskum.
- PRP Ta Yi Gargadi Kan Kafa Sansanonin Sojojin Kasashen Waje A Nijeriya
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 30 Da Wani Malami A Zamfara
Ya rasu ya bar mata uku da ’ya’ya da jikoki da dama.
Marafan Tikau, Alhaji Shaibu Baba Alaraba, ya mika ta’aziyyarsa game da rasuwar sarkin.
Ya bayyana marigayi Sarkin a matsayin “Shugaba nagari kuma mutum mai kima a cikin al’umma, wanda ya kware wajen nuna tausayi, hikima da sadaukar da kai domin jin dadin al’ummarsa.