Shara wata aba ce da ba’a so ko kuma aka gama amfani da ita, shara iri-iri ce, akwai shara daskararriya akwai kuma shara mai ruwa-ruwa.
Yanazu zamani ya canja ana amfani da daskararriyar shara a sarrafa ta zuwa abubuwa masu amfani.
- Iyaye Mu Kara Himmar Samar Da Al’umma Mai Tarin Ilimi –Matar Gwamnan Katsina
- Yaushe Za A Fara Kofin Duniya Na Kungiyoyi?
Kasuwancin sarrafa daskararriyar shara zuwa abin amfani na kawo samu sosai kuma yana rage datti a gari ko kuma wuri. Nijeriya na samun kudi kimanin miliyan talatin da biyu akan sarrafa shara zuwa abu mai amfani. Rashin kayayyakin more rayuwa, rashin doka da kula da gwamnati ke yi ne ya nuna cewa ya kamata masansantun da ba na gwamnati ba su ma su saka hannun jari a ciki.
Bincike ya nuna cewa rashin kula da wasu ‘yan Nijeriya ke yi ta hanyar zubar da shara lokaci ya yi da masu hannun jari za su zo su dauki ragamar abin.
Misali kamfanin Nestle Nigeria bayan samar da daruruwan sana’oí da suka samar wa mutane, ko kuma samo da bubuwan masu amfani, har da tsabtar wuri.
Riba
Za’a iya samun Naira 100,000 kowane wata daga sarrafaffiyar shara kamar su karafa da sauran su.
Amma akan daskararriyar shara, akwai bukatar hannun jari kamar miliyan 4 don sayen motar daukar kayan daskararriyar shara da mobeable mobile toilets.
A wannan lokacin, mai hannun jari a mobile portable toilets zai iya samun dubu biyu kowane rana saboda ana bukatar su sosai a wuraren da ake taron jama’a don yin bukukuwa. Amma a daskararriyar shara za’a bukaci kamar miliyan 4 don sayen motar daukan datti da wasu kayan aiki.