Alkaluma daga ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ko MIIT, sun nuna irin ci gaba bisa daidaito da sashen masana’antun dijital na kasar Sin ya samu a shekarar 2024 da ta gabata, inda a shekarar ta bara sashen ya samu karin kudin shiga da riba.
Alkaluman da MIIT ta fitar a jiya Litinin, sun nuna a baran, sashen ya kudin da ya kai kudin Sin yuan tiriliyan 35, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 4.9, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 5.5 bisa dari a shekara. Kazalika, jimillar ribar da sashen ya samar ta karu da kaso 3.5 bisa dari a shekara, inda ya kai yuan tiriliyan 2.7.
Bugu da kari, a shekarar ta 2024, karin kimar hajoji da manyan masana’antun kirar na’urori masu kwakwalwa ke samarwa, da na na’urorin sadarwa da sauran kayayyakin laturoni, ya karu da kaso 11.8 bisa dari, karin da ya kai na kaso 8.4 bisa dari kan na shekarar da ta gabace ta.
Fannin samar da manhajoji na kasar, shi ma ya samar da karin ribar kaso 10 bisa dari, inda darajarsa ta kai tiriliyan 13.7. Ana kuma danganta ci gaban fannin da fadadar sashen fasahohin kirkirarriyar basira ko AI, da dandalolin adana bayanai, da sauran sassan hada hadar kasuwanci masu alaka da shi. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp