Ministan ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin Yin Hejun, ya ce cikin shekaru biyar da suka gabata, ikon kasar Sin na bunkasa kirkire-kirkiren fasaha ya samu ci gaba bisa daidaito, kana tushen kasar Sin na zama babbar cibiyar harkokin fasaha ya ci gaba da karfafa.
Yin Hejun ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai da ya gudana a Alhamis din nan, inda ya ce a shekarar 2024, adadin kudaden da aka kashe a Sin a fannin bincike da samar da ci gaba mai nasaba da zamantakewar al’umma, ya zarce kudin Sin yuan tiriliyan 3.6, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 506, adadin da ya karu da kaso 48 bisa dari kan na shekarar 2020.
Kazalika, karfin sashen bincike da samar da ci gaba a kasar ya kai kaso 2.68 bisa dari, adadin da ya haura matsakaicin matsayin wanda ake da shi a kasashen tarayyar Turai ta EU. Yayin da kuma jimillar jami’ai dake aiki a wannan fanni na kasar Sin suka kai matsayin farko a duniya.
(Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp