Sashen yawon shakatawa na bangaren teku a kasar Sin ya samu gagarumin ci gaba a rubu’in farko na bana, inda yankunan bakin teku suka nuna bajinta sosai kan harkokinsu, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna.
Kudin da aka samu a sashen ya kai yuan biliyan 384.2 (kimanin dalar Amurka biliyan 53.4) a tsakanin watan Janairu zuwa na Maris, wanda ya karu da kashi 7.5 cikin dari a mizanin shekara-shekara, bisa kididdigar farko da ma’aikatar kula da albarkatun kasa ta kasar Sin ta yi.
- Yunwa Ta Kazanta A Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Tun Bayan Da Majalisar Dinkin Duniya Ta Dakatar Da Ayyukanta
- Seyi Tinubu Ya Musunta Zargin Kamawa Da Bayar Da Cin Hanci Ga Shugaban NANS
Ma’aikatar ta kuma ce, an samu nasarar bullo da sabbin tsarin tafiye-tafiye da yanayin yawon shakatawa, inda suka kara habaka bukatun da ake da su da kuma samarwa a kasuwar yawon shakatawar tekun.
Babban darektan hukumar kula da tattara bayanai da yada su ta bangaren teku ta kasar Sin, Shi Suixiang, ya bayyana cewa, manufofin tallafi da aka bullo da su a matakai na tsakiya da na kananan hukumomi sun karfafa ci gaban yawon shakatawar.
Ya kara da cewa, gwamnatin tsakiya ta inganta fadada hanyoyin jiragen ruwa da kayayyakin yawon shakatawa yayin da kuma ake kara daidaita tsarin rajistar jiragen ruwa da kuma shigar da su cikin hada-hada.
Wasu manazarta dai sun bayyana cewa, a sa’ilin da lokacin goshin damina ke gabatowa, ana sa ran yawon shakatawa na bakin teku da tsibirai a yankin kudu maso gabashin kasar Sin ya bunkasa, tare da kara samun balaguro ta ruwa da nufin cin gajiyar kasuwannin gabashin Asiya da kudu maso gabashin Asiya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp